Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya mamaye Angola, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 kuma ya malale gidaje sama da 4,000, in ji hukumomin gaggawa a ranar Lahadi.
Ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi ya haifar da ambaliyar ruwa wanda ya mamaye tituna kuma ya lalata ababen more rayuwa a babban birnin ƙasar Luanda da kuma birnin Benguela da ke gaɓar tekun Atlantika a kudancin ƙasar.
Benguela ya fi fuskantar ta’adin, inda hukumomin kashe gobara suka ce mutane 12 sun mutu, yayin da uku suka mutu a Luanda, kamar yadda alƙaluman wucin-gadi suka nuna.
"Na rasa kusan komai," a cewar Natalia, wata mazaunin unguwar Kilamba a Luanda.
Ruwa Kogin Zambezi ya karu sosai
Iyalinta sun mayar da 'ya'yanta da jikokinta zuwa wurin 'yan’uwa domin su zauna a can, kamar yadda ta shaida wa AFP.
A makwabtakkiyar kasar Namibia, ruwan Kogin Zambezi ya ƙaru matuƙa, abin da ya tilasta dubban mutanen da ke zama a bakin kogi su bar gidajensu.
Jami'ai sun ce ruwa ya kai kimanin mita 6.8 (ƙafa 22), wanda ya wuce mita 4 na wanda shi ne daidai wa daida.
Hukumomi sun mayar da mazauna zuwa sansanonin wucin gadi guda tara, ciki har da wani sansani wanda ke mutane 2,700, kamar yadda jami'ai suka shaida wa AFP a ranar Asabar.











