| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta yi gargaɗi kan haɗarin kamuwa da sanƙarau a wasu jihohin arewacin ƙasar
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya ta bayyana Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗari na kamuwa da cutar.
Nijeriya ta yi gargaɗi kan haɗarin kamuwa da sanƙarau a wasu jihohin arewacin ƙasar
Zazzaɓi mai zafi da ciwon kai da amai ko wuya ya yi tauri na cikin alamomin cutar. / Reuters
13 Maris 2026

Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta fitar da sanarwar gargaɗi game da lafiyar jama'a inda ta ce akwai jihohin arewacin ƙasar da dama da ke fuskantar ƙarin haɗarin kamuwa da cutar sankarau yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta bayyana cewa cutar sanƙarau wata mummunar cuta ce da ke shafar ƙwayoyin kariya da ke rufe ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma galibi ƙwayar cutar Neisseria meningitidis ce ke haddasa ta.

NiMet ta kuma bayyana cewa cutar na yaɗuwa ta hanyar numfashi daga mutum zuwa mutum, musamman a wuraren da ake cunkoso ko kuma wuraren da iska ba ta shiga yadda ya kamata.

Hukumar ta bayyana Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da Borno a matsayin jihohin da ke cikin babban haɗari na kamuwa da cutar.

Ta kuma buƙaci mazauna yankunan tsakiyar ƙasar da su kasance cikin lura da alamun cutar tare da kai rahoton duk wani zargi kan alamomin cutar da wuri. A halin yanzu, Jihohin Filato, Oyo, Cross River, Edo, Ekiti da Enugu an sanya su cikin yankunan da ba sa ido sosai a kansu.

 “Ku kasance kuna da bayanai. Ku bi shawarwarin hukumomin lafiya kuma ku shiga cikin shirye-shiryen wayar da kan al’umma,” in ji hukumar.

“Ku kare kanku da al’ummarku. Samun bayani da wuri, yin rigakafi, da samun magani da wuri na iya ceton rayuka,” kamar yadda ta ƙara da cewa.

Hukumar ta kuma bayyana cewa duk da cewa cutar na iya tsananta cikin sauri har ta zama barazana ga rayuwa cikin ‘yan sa’o’i idan ba a yi magani ba, gano cutar da wuri da kuma ba da maganin rigakafin ƙwayoyin cutar na iya ƙara yiwuwar a rayu da kuma rage matsalolin da ka iya biyo baya.

NiMet ta ce rukunin waɗanda suka fi fuskantar haɗari sun haɗa da yara da matasa da mutanen da ke rayuwa a wuraren da ke da cunkoso da waɗanda ke fuskantar yanayin zafi da ƙura, da kuma mutanen da garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi.

Alamomin cutar da ya kamata a lura da su sun haɗa da zazzabi mai tsanani da ke zuwa kwatsam da matsanancin ciwon kai, ko wuya ya yi tauri da tashin zuciya ko amai da jin haske yana damun ido.

 

Rumbun Labarai
Nijeriya na neman Turkiyya ta sasanta ta da Nijar don ƙarfafa hadin kai da yaƙi da ta’addanci
An ceto masu ciki da yara da dama daga wurin da ake haifar jarirai a sayar da su a Legas
Sojojin Nijeriya sun kama mutum 14 da ake zargi da satar mai a Jihar Legas
An sace dalibai da ke kan hanyarsu ta zuwa rubuta jarrabawar jami’a a Nijeriya
Harin Kasuwar Jilli ba kuskure ba ne – Ministan Tsaron Nijeriya ya kare matakin rundunar soji
Shuguba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin Nijeriya na 2026, ya tsawaita wa'adin na 2025
Abin da ya sa Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta ce Nijeriya ta shiga yanayi na yaƙi
Nijeriya ta yi gargaɗi kan 'shirin kai harin ta'addanci' kan kayayyakin more rayuwa a Abuja da Neja
Kamfanonin jiragen saman Nijeriya sun yi barazanar dakatar da aiki saboda tashin farashin man jirgi
NACA ta yi gargadi game da yaɗa bayanan HIV ba bisa ƙa'ida ba a shafukan sada zumunta a Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta ce jihohi 33 da al'ummomi 14,000 na cikin hadarin ambaliyar ruwa a 2026
Dakarun Nijeriya sun kai samame a sansanin 'yanta'addan IPOB
'Yansanda a Nijeriya sun kama mutum 33 kan zargin satar mutane a coci
Turkiyya ta raba tallafin tan 36 na abinci ga 'yan gudun hijira a Nijeriya
Tana ƙasa tana dabo game da yiwuwar babban taron Jam'iyyar ADC a Nijeriya
'Yanta'adda sun kai hari sansanin sojin Nijeriya, sun kashe kwamanda da sojoji shida
Nijeriya na neman tallafin IMF da Bankin Duniya don rage tasirin yakin Iran kan tattalin arziki
Me ya sa hare-hare ke karu wa a Nijeriya duk da wanzuwar dakarun Amurka?
Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta soma bincike kan zargin kisan fararen-hula a kasuwar Jilli ta Yobe
ADC ta taya sabbin shugabannin jihohi murna, ta tsayar da ranar 12 ga Mayu don rantsar da su