Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth

Tauraron ɗanwasan Manchester United, Harry Maguire ya samu hukuncin dakatarwar wasa guda da tarar kuɗi daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila, FA, bayan sa'insa da alƙalin wasa.

By
Harry Maguire mai tsaron baya ne da Manchester United ke ji da shi. / Reuters

Hukumar FA ta Ingila ta hukunta Harry Maguire na Manchester United, bayan gudanar da bincike kan halayyar da ya nuna a wasan United da Bournemouth ranar 20 ga Maris a gasar Firimiya.

Bayan jan katin da aka bai wa ɗanwasan a minti 78 na wasa, FA ta same shi da laifin rashin ɗa’a, kuma ta dakatar da shi wasa guda da kuma tarar kuɗi.

Mai shekaru 33, Maguire ya yi martani cikin fushi kan ɗaya cikin alƙalan wasan, mai suna Matt Donohue, bayan da aka ba shi jan kati.

An zarge shi da zagin alƙalin kuma bayan gudanar da bincike, Harry Maguire ya amsa laifinsa.

Wata sanarwa daga FA ranar Laraba, ta tabbatar da hukuncin da cewa, "Kwamitin Kiyaye Doka mai zaman-kansa ya ɗora dakatarwa wasa guda da tarar fam £30,000 kan ɗanwasan Manchester United FC, Harry Maguire”.

Dakatarwar za ta hana shi buga wasan da United za ta kara da Chelsea a ƙarshen mako. Kuma tuni da ma ya rasa wasan da United ta faɗi da ci 2-1 a hannun Leeds United saboda jan katin.