Gobara ta ci gaba da balbala a kan wani jirgin ruwa dauke da LPG mai tutar Turkiyya, wanda wani abu ya fado masa a tashar jiragen ruwa da ke Odessa a Ukraine, in ji Muhittin Celik, jakadan karamin ofishin jakadancin Turkiyya da ke garin na kudancin Ukraine.
Jirgin ruwan mai tutar Turkiyya ORINDA, dauke da man LPG ya fuskanci lamarin yayin da yake sauke kaya a tashar jiragen ruwa ta Izmail, Celik ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu, kuma ya ambaci cewa an kwashe dukkan ma'aikatan jirgin kuma suna cikin koshin lafiya, duk da cewa akwai yiwuwar samun fashewa.
Celik ya ce jirgin sama marar matuki (UAV) ne ya janyo hatsarin, wanda ya faru a safiyar Litinin din nan.
"Ma'aikatan jirgin sun tuntubi wayar tarho din ofishin jakadancinmu da ke aiki kuma sun ba da rahoton halin da ake ciki.
“Ma'aikatan ofishin jakadancinmu sun yi aiki tare da hukumomin yankin kuma sun tabbatar da bayar da kariya daga ofishin jakadancin ga lafiyar ma'aikatan jirgin," in ji shi.
Ya kara da cewa ma'aikatan jirgin 16 na cikin koshin lafiya. Kashi biyu bisa uku na gas din har yanzu na cikin jirgin. Ma'aikatan kashe gobara sun yi kokarin kashe wutar ta hanyar fesa ruwa.
Ya ƙara da cewa an ƙara daukar matakan tsaro a tashar jiragen ruwa saboda hatsarin fashewar wani abu da za a iya samu.
"Dangane da rahoton tawagar da ta fito daga Turkiyya, za a tantance ko za a iya sake amfani da jirgin."
Babban Daraktan Harkokin Ruwa na Ma'aikatar Sufuri da Kayayyakin more rayuwa ta Turkiyya ya sanar da cewa jirgin yana ɗauke da ma'aikata 16 na Turkiyya, kuma gobara ta tashi yayin sauke kaya a Tashar Jirgin Ruwa ta Izmail ta Ukraine.
















