| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban majalisar dokokin Turkiyya ya yi kira da a dakatar da Isra'ila daga MDD
Numan Kurtulmus ya yi kira da a dakatar da Isra'ila kan ƙudirin doka ta hukuncin kisa ga Falasɗinawa fursunoni, yana mai ishara ga Afirka ta Kudu a lokacin mulkin wariyar launin fata.
Shugaban majalisar dokokin Turkiyya ya yi kira da a dakatar da Isra'ila daga MDD
Kurtulmus ya ce Isra'ila daidai take da Afirka Ta Kudu a lokacin mulkin wariyar launin fata a kiran da ya yi ga MƊD ta dakatar da ita / AA
4 awanni baya

Shugaban majalisar dokokin Turkiyya Numan Kurtulmus ya yi kira da a dakatar da Isra’ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), yana mai sukar ƙoƙarin ayyana ƙudirin hukuncin kisa kan fursunoni Falasɗinawa inda yake ishara ga matakin ƙasashen duniya kan Afirka ta Kudu a zamanin mulkin wariyar launin fata a matsayin hujja.

Da yake jawabi a taro na 152 na hukumar haɗaka ta majalisun dokoki ta duniya (IPU) a birnin Istanbul, Kurtulmus ya ce tsarin ƙasa da ƙasa ya ɗauki mataki kan mulkin wariyar launin fata a baya, inda ya tuna da dakatar da Afirka Ta Kudu daga MƊD a shekarar 1974.

Ya ce Isra’ila tana aikata irin waɗannan ɗabi’un, inda yake tambaya cewa : "Shin ba mulkin wariyar launin fata ba ne a yi amfani da wata doka ta daban kan Falasɗinawa kuma a yi amfani da wata doka ta daban kan Isra’ilawa a cikin ƙasa ɗaya ?"

Kurtulmus ya kuma soki MƊD, yana mai cewa ta gaza hana rikice-rikice na baya bayan nan kuma ta kasa wajen hana tashin hankali, musamman a Gaza.

"Abin taƙaici, MƊD ta kasance hukuma ta ƙasa da ƙasa wadda ke aiki bisa muradun waɗanda ke riƙe da iko," in ji shi.

Kira don gyara

Da yake bayyana cewa ƙasashe da yawa a Gabas Ta Tsakiya suna fama da ƙeta ‘yancin kansu, Kurtulmus ya jaddada cewa duk ƙasashen duniya suna da ‘yanci na bai ɗaya.

A gefe ɗaya kuma, ya gana da Khalid Al Maawali, shugaban majalisar Shura ta ƙasar Oman, yana mai godiya ga ƙasar Oman kan ƙoƙarinta na shiga tsakani kuma yana kira da a sake fara tattaunawa a Pakistan domin mayar da tsagaita wutan na dindindin.

Ya yi gargaɗin cewa matakan Isra’ila na barazanar ruruta wutar adawa tsakanin ƙasashen Larabawa na gaɓar teku da Iran .

Kurtulmus ya ce Turkiyya tana karɓar baƙuncin taron hukumar haɗaka ta majalisun dokoki ta duniya IPU a karo na huɗu ne , inda kimanin ƙasashe 155 suka sami wakilci a Istanbul.