| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Shugaban Iran Pezeshkian ya bayyana tattaunawar nukiliya da Amurka a matsayin 'ci gaba' ga Tehran
Jami’an Iran da Amurka sun nuna alamun samun ci gaba a tattaunawar nukiliya inda ska amince cewa akwai yiwuwar ci gaba da tattaunawa nan gaba a Muscat da ke Oman.
Shugaban Iran Pezeshkian ya bayyana tattaunawar nukiliya da Amurka a matsayin 'ci gaba' ga Tehran
Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian yana magana yayin wani taro / Reuters
9 Fabrairu 2026

Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka , wadda aka yi da taimakon ƙasashen yanki, ta nuna alamun “ci-gaba,” kamar yadda Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana ranar Lahadi.​​

“Tun da can tattaunawa ita ce dabararmu ta samun mafita ta lumana ,” kamar yadda Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na shafin sada zumunta na X, yana mai jaddada cewa hanyar da Iran ta bi kan batun nukiliya ta dogara ne kan “‘yancin da aka tabbatar a yarjejeniyar hana yaɗuwar makamin nukiliya.”

Shugaban na Iran ya ƙara da cewa ƙasar “tana mayar da martani ga girmamawa da ladabi, amma ba ta lamuntar kalaman tilastawa.”

Iran da Amurka sun soma harkar diflomasiyyar nukiliya a kaikaice ranar Juma’a bayan makonni na tashin hankali, wanda barzanar matakin sojin Shugaban Amurka Donald Trump kan ƙasar ta yi ta yi.

Minsitan Harkokin Waje Abbas Araghchi ya bayyana tattaunawar a matsayin wani “mafari mai kyau,” yana mai cewa za su iya ci gaba idan aka shawo kan yanayin rashin aminci.

Ya ce an amince cewa za a ci da bin matakin da kuma cewa ɓangarorin biyu za su sake haɗuwa a Muscat, Oman, nan gaba.

Araghchi ya bayyana cewa shirin makami mai linzamin Iran ba zai kasance ƙarƙshin ko wace tattaunawa ba a yanzu ko kuma a nan gaba, yana mai bayyana shi a matsayin “harkar tsaro.”​​​​​​

Rumbun Labarai
Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila bayan Trump ya yi iƙirarin daƙile ƙarfin sojinta
Isra’ila ce ummul aba'isin haramtaccen yaƙi da Iran: In ji Erdogan na Turkiyya
Kalin ya karɓi baƙuncin tawagar Hamas don tattauna shirin zaman lafiya na Gaza
Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3
Iran ta ce lokaci ya yi da Saudiyya za ta kori sojojin Amurka daga yankinta
Yadda yaƙin Iran zai iya rikita kasuwancin duniya ta Mashigar Teku ta Bab al Mandeb
Ubangiji ba ya karɓar addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi - Fafaroma
Trump na son ƙwace man Iran, ya sa ido a Tsibirin Kharg yayin da dakarun Amurka ke son shiga— rahoto
Pentagon na shirya jadawalin ayyukan sojin ƙasan Amurka na tsawon makonni a Iran — Rahoto
Iran ta kai hari sansanin soji a Saudiyya, ta jikkata sojin Amurka 12, ta lalata jirage da dama
Trump ya dakatar da hari kan tashoshin makamashin Iran na kwana 10, ya ce ana 'ci gaba' da tuntuɓa
Netanyahu ya bayar da umarnin ƙara zafafa hari kan Iran saboda tsoron Trump na iya dakatar da yaƙin
Jamus ta soki yaƙin Isra'ila da Amurka kan Iran, ta ce 'babu dabarar ficewa'
Isra'ila na dab da halasta hukuncin kisa kan fursunoni Falasɗinawa
Hatsarin Nukiliya:  Shin yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran zai iya janyo harba nukiliya?
Iran na neman kafa ƙawancen soji a yankin Gabas ta Tsakiya ban da Amurka da Isra’ila
Isra'ila ta yi asarar $57bn a tattalin arzikinta cikin shekara biyu kan kisan kiyashin Gaza
Sojojin Isra'ila sun azabtar da yaro ɗan shekara ɗaya don tilasta wa mahaifinsa amsa tambayoyi
Ƙasashen Larabawa da ke gaɓar teku sun nuna goyon baya ga Turkiyya, Qatar bayan hatsarin helikwafta