Turkiyya da Saudiyya sun jaddada goyon bayansu ga haɗin kan Somaliya da zaman lafiyar yankin
Shugabannin ƙasashen Turkiyya da Saudiyya sun jaddada matsayarsu ta adawa da ƙungiyoyin ‘yan a-ware da tsarin raba ƙasar da ke yankin Kusurwar Afirka a yayin ganawar da suka yi a birnin Riyadh.
Turkiyya da Saudiyya sun jaddada goyon bayansu ga iko da kuma ‘yancin Somaliya, inda suka yi watsi da abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin raba kan ƙasar da kuma tsarin da ke barazana ga haɗin kan Somaliya wacce ke yankin Kusurwar Afirka.
Hakan na daga cikin batutuwan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a Riyadh a yayin ziyarar aiki ta kwana ɗaya da ya kai ƙasar.
A cewar wata sanarwa da Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar a ranar Laraba, shugabannin biyu a ranar Talata sun jaddada "goyon bayansu" ga haɗin kan Jamhuriyar Tarayyar Somaliya da zaman lafiya da ci gaba da kuma walwalar al'ummarta.
Sun kuma yi Allah wadai da sanarwar amincewa da juna tsakanin hukumomin Isra'ila da na yankin Somaliland, suna masu cewa hakan yana ƙarfafa matakan raba ƙasar tare da karya dokokin ƙasa da ƙasa, da kuma ta'azzara rikicin yankin.
A ƙarshen watan Disamban bara ne Isra'ila ta sanar da cewa ta amince da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Somaliland ta kasance ƙasa mai cin gashin kanta tun bayan ayyana samun 'yanci daga Somaliya a shekarar 1991. Ta gaza samun amincewar ƙasashen duniya, yayin da gwamnatin tarayya ƙasar ta jadadda cewa yankin muhimmin ɓangare ne na ƙasarta.
Tallafin haɗin gwiwa ga halastacciyar gwamnati a Yemen
A ɓangare guda, Ankara da Riyadh sun jaddada goyon bayansu ga halastacciyar gwamnatin Yemen wadda Majalisar gwamnatin Shugaban ƙasa ke wakilta, sannan sun yi nuni kan muhimmancin kare ‘yanci da haɗin kai da kuma haƙƙin iko na Yemen.
Turkiyya ta bayyana goyon bayanta ga rawar da Saudiyya ke takawa a Yemen da kuma ƙoƙarin da shugaban Majalisar Shugabancin yankin ke yi wajen warware rikicin da kuma ci gaba da sulhu, gami da kiran babban taro a Riyadh wanda ya haɗa dukkan ƙungiyoyin kudancin yankin.
Kiyaye haɗin kan Sudan
Kan batun Sudan kuwa, ƙasashen biyu sun bayyana matsayinsu na tsayin daka ga kiyaye haɗin kan Sudan da tsaro da kuma ‘yancinta, yayin da suka yi watsi da duk wani tsari haramtacce daga hukumomin da doka ba ta san da su ba a ƙasar.
Sun kuma jaddada buƙatar hana Sudan zama cibiyar rikici, da daƙile miyagun ayyuka da kuma kwararar makamai daga ƙasashen waje ba bisa ƙa'ida ba, yayin da suka yi kira da a kare fararen-hula da kuma isar da agajin jinƙai ba tare da wata matsala ba bisa tsarin dokokin jinƙai na duniya da kuma yarjejeniya Jeddah ta watan Mayun 2023.
Turkiyya ta yaba da koƙarin Saudiyya na taimakawa wajen ganin an kawo ƙarshen yaƙin da kuma rage wa al'ummar Sudan raɗaɗi tashin hankalin, yayin da Riyadh ta nuna godiya ga irin taimakon jinƙai na Turkiyya.
Duka ɓangarorin sun yi maraba da shawarar da Rundunar Sojin Sudan ta yanke ta ci gaba da buɗe hanyar tsallaka iyakokin yankin Adre da Chadi na tsawon lokaci da kuma sake buɗe filayen jiragen sama da sauran iyakokin shiga ƙasar da dama don sauƙaƙa isar da kayayyakin jinƙai.
Erdogan, Yarima mai jiran gado na Saudiyya sun yi kira da a janye Isra'ila daga Syria
A kan Syria, Ankara da Riyadh sun yaba da abin da suka kira matakan da gwamnatin Siriya ta ɗauka na kiyaye tsaro, da kwanciyar hankali da kuma mutuncin yankunanta, kana sun yi maraba da ƙoƙarin ƙasa da ƙasa na tallafa wa Damascus da kuma ɗage takunkuman da aka ƙaƙaba mata.
Sun bayyana goyon bayansu ga yarjejeniyar tsagaita wuta da haɗewar ƙasar ta ranar 30 ga watan Janairu, sun kuma jaddada goyon bayansu ga ƙoƙarin yakar ƙungiyoyin 'yanta'adda da kuma inganta zaman lafiya, sannan sun yin Allah wadai da yanda Isra’ila ta yi ta keta haƙƙokin ikon Siriya.
Ɓangarorin biyu sun sabunta kiraye-kirayensu kan janye Isra'ila daga dukkan yankunan Syria da ta mamaye nan-take, inda suka yi gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-haren Isra’ila na kawo cikas ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma barazanar ta'azzara rikici a yankin.