Masu haƙar ma'adinai 38 ne suka mutu lokacin da tukunyar gas ta fashe a wani wajen haƙar ma’adanai a jihar Filato da ke yankin tsakiyar Nijeriya, kamar yadda majiyoyin yankin suka shaida wa AFP.
Wasu mutum 27 ɗin kuma sun ji raunuka a fashewar da ta faru a wurin haƙar ma'adinai na Kampanin Zurak da ke gundumar Bashar ta jihar Filato, kamar yadda muƙaddashin sarkin gargajiya na yankin ya gaya wa AFP.
"Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 38, kuma an garzaya da kimanin mutane 27 zuwa asibiti," in ji shugaban, Alhaji Aliyu Adamu Idris.
Ibrahim Dattijo Sani, wani ma'aikacin hakar ma'adinai a wata mahaƙa da ke kusa, ya shaida wa AFP cewa wadanda abin ya shafa suna karkashin kasa a cikin mahaƙar da fashewar ta faru tsakanin karfe 7:30 zuwa 8:00 na safe (06:30 da 07:00 GMT).
"Muna kusa da wuraren, mutane suna cikin wajen hakar ma'adinai kuma ba zato ba tsammani sai tukunyar gas ta fashe," in ji Sani.
"Mun yi ƙoƙari sosai don ceto amma abin takaici mutum 38 sun mutu... an kai wasu asibiti."
Wani rahoton sirri na tsaro da AFP ta gani ya danganta mutuwar masu hakar ma'adinan da shaƙar "gubar carbon monoxide".
Zurak wani tsohon wurin hakar ma'adinai ne a ƙaramar hukumar Wase. Idris ya shaida wa AFP cewa wurin da fashewar ta faru yana karkashin ikon Kamfanin Solid Unit Nigeria Limited.
Jihar Filato waje ne na tarihi na haƙar ma'adinai, inda babban birninta Jos aka fi sani da birnin Tin. Amma ayyukan haƙar ma'adinai sun ragu a cikin 'yan shekarun nan.
A baya ma an sha samun irin wannan hatsarin a Nijeriya.
Akalla mutum 18 ne suka mutu a jihar Zamfara da ke arewa maso yamma bayan wani dutse ya fado kan wani ma'adinan da ba bisa ka'ida ba a lokacin ruwan sama mai karfi a watan Satumba.
Hukumomi a ƙasar sun ɗora alhakin hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da ke ƙara ta'azzara ta'addancin 'yan fashi, inda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke samun kuɗi daga kuɗaɗen fansa da suke karɓa daga masu haƙar ma'adinai.












