TURKIYYA
2 minti karatu
Turkawa 36 da Isra'ila ta kama a cikin jirgin ruwan Global Sumud Flotilla za su koma gida Turkiyya
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ya ce suna ci gaba da bin matakai domin sakin sauran Turkawan da Isra'ila ta kama a cikin teku.
Turkawa 36 da Isra'ila ta kama a cikin jirgin ruwan Global Sumud Flotilla za su koma gida Turkiyya
Sumud flotilla
4 Oktoba 2025

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana cewa, 'yan kasar Turkiyya 36 da sojojin Isra’ila suka kama a cikin jiragen ruwan Global Sumud Flotilla a cikin tekun duniya za su koma gida, Turkiyya da yammacin yau ta jirgi na musamman.

“Adadin karshe bai tabbatar ba tukuna. Muna ci gaba da ƙoƙarin kammala dukkan matakan da suka dace don ganin sauran 'yan kasarmu sun dawo gida cikin gaggawa,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a shafinsa na X a ranar Asabar.

Ya ƙara da cewa jirgin da aka shirya zai kuma dauki wasu 'yan kasashen waje.

An kama masu fafutuka fiye da 470

Kungiyar Freedom Flotilla Coalition, wata gamayyar ƙungiyoyin al’umma ta ƙasa da ƙasa, ta sha yunƙurin ratsa ƙawanyar da aka yi wa Gaza tun daga shekarar 2010 don jawo hankalin duniya kan matsalar jin kai a yankin.

Sojojin ruwa na Isra’ila sun kai hari tare da ƙwace jiragen ruwan Global Sumud Flotilla a ranar Alhamis, inda suka kama masu fafutuka fiye da 470 daga ƙasashe fiye da 50.

Jiragen sun yi ƙoƙarin kai tallafin jin ƙai zuwa Gaza da kuma ƙalubalantar takunkumin da Isra’ila ta ƙaƙaba wa yankin.

Isra’ila ta ci gaba da yi wa Gaza ƙawanya, inda mutane kusan miliyan 2.4 ke zaune, tsawon kusan shekaru 18. Tun daga watan Oktoban 2023, hare-haren bama-baman Isra’ila sun kashe kusan Falasɗinawa 66,300 a yankin, yawancinsu mata da yara, tare da sanya yankin cikin mawuyacin hali, yayin da takunkumin ya jefa Gaza cikin yunwa.

Rumbun Labarai
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista
Turkiyya na da rawar da za ta taka a tsaron Turai, ta shirya domin aikin Gaza: Ministan Tsaro
Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin TRCN kan ƙudurin samar da ƙasashe biyu
Ya kamata amincewar Ƙasashen Yamma da Falasɗinu ta zama silar samar da mafita ta ƙasa biyu: Erdogan
Jami'an Turkiyya da Syria sun gudanar da tattaunawa kan tsaro a Ankara