Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102

Yayin da ake bukukuwa a duk fadin Turkiyya don cika shekara 102 da zama jamhuriyya, 'yan ƙasa sun nuna farin ciki da murna a duk faɗin kasar.

Turkish flags are hung on the Fatih Sultan Mehmet Bridge to mark the 102nd anniversary of Turkish Republic Day in Istanbul, Türkiye. / AA

A ranar 29 ga Oktoba, 2025, Turkiyya ta yi bikin cika shekaru 102 da zaman ƙasar Jamhuriya, inda aka tuna lokacin da Mustafa Kemal Atatürk, wanda ya kafa Turkiyya ta zamani, ya ayyana ƙasar a matsayin Jamhuriya.

A duk faɗin ƙasar, birane suna gudanar da bukukuwa cike da nuna ƙaunar ƙasa, da jerin gwano, da nune-nunen tarihi da ke sa 'yan ƙasa jin alfahari da farin ciki.

Tafiyar shekaru ɗari ta Turkiyya tana cike da nasarori masu ban mamaki a fannin kimiyya, fasaha, da haɗin kai ƙasa, inda ake girmama tarihi mai daraja yayin da ake fatan kyakkyawar makoma.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan, tare da rakiyar manyan jami'an gwamnati, sun ziyarci Anıtkabir don bikin Ranar ta Jamhuriyar Turkiyya ta 29 ga Oktoba.

Bayan sanya furanni mai ɗauke da tauraro da wata a kan hubbaren Atatürk, Erdogan da jami'an sun yi shiru na ɗan lokaci, sannan aka rera taken ƙasar.

Tawagar jiragen sama masu ban sha'awa na Sojojin Sama na Turkiyya, SOLOTURK, sun yi nuni mai ban sha’awa a yanki mai tarihi da UNESCO ta ayyana a Pamukkale da ke lardin Denizli, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Ranar Jamhuriyar Turkiyya na ranar ta 29 ga Oktoba.

Masu nutso na Sashen 'Yan Sandan Turkiyya sun ɗaga tutar ƙasa a jikin ragowar jirgin Monem, wanda ya nutse a kusa da Cesme a shekarar 2004 yayin da ake jan shi zuwa Aliaga don a kwanshe shi, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 102 na Jamhuriyar Turkiyya.

A Igdır, da ke yankin Gabashin Anatolia na Turkiyya, ɗaliban Makarantar Firamare ta Inonu sun jeru inda suka rubuta “Shekara ta 102” a filin makarantarsu don bikin Ranar Jamhuriyar da cika shekaru 102 da kafa Jamhuriyar.