Isra'ila ta kashe fararen-hula 114 a Lebanon bayan saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta: MDD
Mai magana da yawun ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na MDD ya ce ofishin na bibiyar farmakin jiragen sama na Isra'ila a kan gine-gine a ƙauyukan da ke kudu, ya kuma ce mutuwar fararen-hula ta ci gaba da ƙaruwa tun lokacin da aka tsagaita wuta.
Ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta ta Nuwamba 2024 da Isra'ila ta yi a Lebanon ya haifar da mutuwar fararen-hula 114.
Mai magana da yawun ofishin, Thameen Al-Kheetan, ya bayyana wa Anadolu cewa ofishin na bibiyar farmakin jiragen sama na Isra'ila a kan gine-gine a ƙauyukan da ke kudu, ya kuma ce mutuwar fararen-hula ta ci gaba da ƙaruwa tun lokacin da aka tsagaita wuta.
Ya jaddada cewa dole ne a dakatar da kisan da ake ci gaba da yi wa fararen-hula "nan take", yana mai cewa mazauna yankin sun yi rayuwa cikin rashin tabbas da fargaba fiye da shekaru biyu.
Haka kuma ya yi kira da a gaggauta bin yarjejeniyar dakatar da tashin hankali da kuma dokokin jinƙai na kasa da kasa.
Sojojin Isra'ila sun kashe fiye da mutum 4,000 kuma sun jikkata kusan 17,000 a hare-harensu kan Lebanon, wanda suka fara kaiwa tun Oktoban 2023 inda zuwa Satumban 2024 hare-haren suka ƙazanta.