'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 30 a Jihar Neja ta Nijeriya, sun ƙona ofishin 'yansanda
Rahotanni sun ce 'yanbindigan sun kai harin ne kan ƙauyuka uku inda suka ƙona gidaje da shaguna da tilasta wa mutane barin ƙauyukan, inda wani mazaunin Tunga-Makeri ya tabbatar da cewa 'yanbindigar sun yanke kan mutane shida.
‘Yanbindiga ɗauke da makamai a kan babura sun kashe aƙalla mutane 30 tare da kona gidaje da shaguna yayin hare-hare kan kauyuka uku a Jihar Neja ta Nigeria da safiyar ranar Asabar, kamar yadda mazauna yankin da suka tsira daga harin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Hare-haren da aka kai kan kauyukan da ke Karamar Hukumar Borgu, kusa da iyaka da Jamhuriyar Benin, na daga cikin yawaitar hare-haren ‘yanbindiga ke kaiwa wadanda ke garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma raba al’umma da muhallansu a arewacin Nijeriya.
Kakakin rundunar ‘yansanda a Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin da aka kai a ɗaya daga cikin ƙauyukan.
“’Yanbindigan da ake zargi sun kai hari ƙauyen Tunga-Makeri… mutane shida sun rasa rayukansu, an kuma kona wasu gidaje, sannan an sace wasu mutane da har yanzu ba a tantance adadinsu ba,” in ji Abiodun.
Ya ƙara da cewa maharan sun wuce zuwa ƙauyen Konkoso, yayin da bayanai kan sauran hare-haren ba su fito fili ba.
Jeremiah Timothy, wani mazaunin Konkoso da ya tsere zuwa wani ƙauye na kusa, ya ce harin ƙauyensu ya fara da sassafe tare da harbe-harbe ba kakkautawa.
“Akalla mutane 26 aka kashe ya zuwa yanzu a kauyen bayan da suka kona ofishin ‘yansanda,” in ji Timothy, yana mai cewa maharan sun shiga Konkoso da misalin karfe 6:00 na safe, suna harbe-harbe.
Ya ce mazauna yankin sun ji jiragen yakin soja yana shawagi a sararin samaniya.
Wani wanda ya shaida lamarin ya bukaci a sakaya sunansa ya ce maharan, wadanda suka zo kan babura fiye da 200, sun mamaye yankin suna kai hari kan kauyukan.
Auwal Ibrahim, wani mazaunin Tunga-Makeri, ya bayyana cewa maharan sun kai hari kauyensu da sassafe, kusan karfe 2:00 na dare agogon GMT.
“‘Yan bindigar sun kutsa cikin garinmu da misalin karfe 3:00 na dare kan babura da yawa suna harbe-harbe ba kakkautawa, sun yanke kan mutane shida tare da kashe wasu. Sun kona shaguna kuma suka tilasta wa ɗaukacin kauyen tserewa,” in ji Ibrahim.
Ya kara da cewa da dama daga cikin mazauna yankin na tsoron komawa gidajensu saboda har yanzu maharan na kusa da yankin.