Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma ƙarƙashin Operation Fansan Yamma sun kashe wasu da ake zargin ’yanta’addan Lakurawa ne guda biyu tare da ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka kai a Jihar Kebbi, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.
An gudanar da samamen ne a ranar 27 ga Yuni a yankin Sabarumawa, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na tarwatsa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke kai hare-hare a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
A cewar rundunar sojin, an ƙaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa waɗanda ake zargin na shirin kai hari kan al’ummar Sabarumawa. Daga nan ne aka tura dakarun Bataliya ta 7 ta Shirin Shiga Tsakani ta Babban Hafsan Sojin Ƙasa zuwa yankin, inda suka yi kwanton-ɓauna a wata hanya da ake kyautata zaton maharan za su bi.
Rundunar ta ce dakarun sun yi musayar wuta da maharan yayin da suke kusantar wurin kwanton-ɓaunar, lamarin da ya yi sanadin kashe ’yanta’adda biyu, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin dazukan da ke kusa.
Bayan gudanar da bincike a yankin, jami’an tsaron sun ƙwato bindigogin AK-47, jigidun harsasai, da harsasai 143 da kuma babur guda ɗaya.
Dakarun Operation Fansan Yamma sun ce sun ce wannan samame na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsaro da kuma tarwatsa ƙungiyoyin ’yanta’adda da masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa ayyukan yaƙi da ta’addanci da ake ci gaba da gudanarwa.










