| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
“A kowace rana mutane na mutuwa … kuma hakan na faruwa kusan tsawon mako guda. A rana guda muna binne mutane biyu, uku, ko ma fiye da haka,” in ji Jean Marc Asimwe, wani mazaunin Bunia. “A wannan lokaci, ba mu san wace irin cuta ba ce,” in ji Asimwe.
Mutum 80 sun rasu a sabuwar ɓarkewar Ebola a Jamhuriyar Congo
Tsohuwar ajiya: Ma'aikatan lafiya yayin da suke shirin binne wata gawa da Ebola ta kashe a Jamhuriyar Kongo a 2019. / Reuters

Akalla mutane 80 ne aka ruwaito sun mutu a sabuwar ɓarkewar cutar Ebola a lardin Ituri da ke gabashin Congo, in ji jami’ai, yayin da ma’aikatan lafiya suka duƙufa a ranar Asabar wajen ƙara bincike da bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da masu cutar domin daƙile yaɗuwar ta.

Jami’ai sun fara sanar da ɓarkewar cutar ne a ranar Juma’a, inda aka ce mutane 65 sun mutu sannan akwai mutane 246 da ake zargin sun kamu.

A halin da ake ciki, ‘yan jaridar kamfanin dillancin labarai na Associated Press a Bunia, babban birnin Ituri, sun tattauna da mazauna yankin da suka bayyana fargabarsu da yadda ake yawan jana’iza.

“A kowace rana mutane na mutuwa … kuma hakan na faruwa kusan tsawon mako guda. A rana guda muna binne mutane biyu, uku, ko ma fiye da haka,” in ji Jean Marc Asimwe, wani mazaunin Bunia. “A wannan lokaci, ba mu san wace irin cuta ba ce,” in ji Asimwe.

Ministan Lafiya na Congo, Samuel-Roger Kamba a ranar Jumma’a ya ce an tabbatar da mutane takwas sun kamu da cutar ta hanyar gwajin dakin gwaje-gwaje, ciki har da mutum huɗu da suka mutu.

Sakamakon gwaje-gwaje ya tabbatar da cewa cutar ita ce kwayar Bundibugyo, wani nau’in Ebola da bai fiye bayyana ba a ɓarkewar cututtukan Ebola na baya a Congo. Wannan ita ce ɓarkewar Ebola ta 17 a Congo tun bayan da aka fara gano cutar a ƙasar a shekarar 1976.

Cuta mai saurin yaɗuwa

Ebola cuta ce mai matuƙar saurin yaɗuwa kuma ana iya kamuwa da ita ta hanyar ruwan jiki kamar amai, jini, ko maniyyi. Cutar da take haifarwa ba kasafai ake samu ba, amma tana da tsanani kuma galibi tana kashe mutum.

Kamba ya ce wadda ake zargin ita ce farkon wadda ta kamu a wannan sabuwar ɓarkewar wata ma’aikaciyar jinya ce da ta mutu a wani asibiti a Bunia. Ya ce lamarin ya fara ne tun makonni uku da suka gabata, ranar 24 ga Afrilu.

Bai bayyana ko an gwada samfurin jikin ma’aikaciyar jinyar ba, amma ya ce tana nuna alamomin da ke kama da Ebola.

Congo babbar ƙasa ce da sau da yawa ke fuskantar ƙalubalen sufuri da kayan aiki. Duk da cewa ƙasar na da ƙwarewa wajen magance barkewar Ebola, tana yawan fuskantar matsalolin kai kwararru da kayan agaji zuwa yankunan da cutar ta shafa.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da cutar a yankunan uku a lardin Ituri, ciki har da babban birnin Bunia, da kuma Rwampara da Mongwalu inda barkewar cutar ta fi ƙamari.

Uganda ma ta tabbatar da samun mutum ɗaya da ya kamu da Ebola wanda jami’ai suka ce an “shigo da” cutar daga Congo. Mutumin ya mutu a wani asibiti a Kampala, babban birnin Uganda.