| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Binciken zai fi mayar da hankali ne kan kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan yaƙi da cutar HIV da tarin fuka a ƙarƙashin shirye-shiryen da Hukumar Raya Ƙasa ta Amurka (USAID) ke aiwatarwa.
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
FBI ta ce an fara samun damuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen USAID a shekarar 2025

Ofishin Binciken Laifuka na Amurka (FBI) ya nemi haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC) wajen gudanar da bincike kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen da gwamnatin Amurka ta samar a ƙarƙashin shirye-shiryen da take tallafawa.

Macus Maccain, wanda shi ne mataimakin jami’in hulɗa da hukumomin yaƙi da laifuka na FBI, ne ya gabatar da wannan buƙata yayin ziyarar da ya kai ofishin mukaddashin daraktan shiyyar EFCC a Legas, Bawa Kaltungo.

Binciken zai fi mayar da hankali ne kan kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan yaƙi da cutar HIV da tarin fuka a ƙarƙashin shirye-shiryen da Hukumar Raya Ƙasa ta Amurka (USAID) ke aiwatarwa.

FBI ta ce an fara samun damuwa ne bayan da gwamnatin Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen USAID a shekarar 2025, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan kuɗaɗen da suka rage hannun ƙungiyoyin da ke aiwatar da shirye-shiryen.

Ana zargin wasu daga cikin ƙungiyoyin da yin almundahana ko karkatar da kuɗaɗen kafin a dakatar da shirye-shiryen.

Jeremy Kennon, wani jami’in bincike na musamman daga Ofishin Babban Sufeton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ya ce binciken da aka gudanar ya kuma gano damuwa kan hauhawar kasafin kuɗi da wasu matsalolin kuɗi a Kano da wasu jihohin Nijeriya.

Kaltungo ya tabbatar wa tawagar FBI cewa EFCC za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen a dukkan jihohin da ƙungiyoyin da shirye-shiryen da abin ya shafa suka gudanar da ayyukansu, tare da bin diddigin yadda kuɗaɗen suka fita har zuwa ga waɗanda suka amfana da su.

Ya kuma yi maraba da shirin kafa dangantakar aiki ta dogon lokaci tsakanin hukumomin biyu, ciki har da musayar bayanan sirri da bayanan da suka shafi bincike.

Gwamnatin Trump ta rufe USAID a watan Yulin 2025, lamarin da ya kawo ƙarshen ayyukan raya ƙasa na duniya da hukumar ta kwashe fiye da shekaru sittin tana gudanarwa.