| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
UEFA ta fara bincike kan cin zarafin Vinicius Jr da ɗanwasan Benfica ya yi
Bayan zargin da ɗanwasan Real Madrid, Vinicius Jr ya yi kan cewa ɗanwasan Benfica, Gianluca Prestianni ya ci zarafinsa, hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA ta sanar da ƙaddamar da bincike kan batun wariyar launin fata.
UEFA ta fara bincike kan cin zarafin Vinicius Jr da ɗanwasan Benfica ya yi
UEFA ta fara bincike kan cin zarafin Vinicius Jr da ɗanwasan Benfica ya yi / Reuters
7 awanni baya

Wasan gasar Zakarun Turai na maraicen Talata tsakanin Real Madrid da Benfica ya bar baya da ƙura, inda zuwa yanzu hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA ta tabbatar da cewa ta fara gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a wasan.

Yayin wasan na cike gurbi a gasar Zakarun Turai, tauraron ɗanwasan Madrid, Vinicius Jr ya yi ƙorafin cewa ɗanwasan gaban Benfica, Gianluca Prestianni ya masa zagin launin fata.

A yanzu dai tuni hukumar UEFA, ta sanar da cewa ta miƙa wa kwamitinta na ladabi da ladabtarwa ya duba lamarin da ya faru a filin wasa na Estadio da Luz, inda Madrid ta doke Benfica da ci 1-0.

Lamarin ya auku ne jim-kaɗan bayan Vinicius Jr ya zura ƙwallo, kuma bayan faruwar lamarin an kwashe mituna 10 ana cecekuce, inda tarin ‘yanwasa suka yi sa-in-sa da alƙalin wasa.

Bayan cin ƙwallo, an ga Vinicius ya ruga wajen alƙali yana mai zargin Prestianni da faɗa masa kalaman zagin launin fata. Alƙali, Francois Letexier, ya ɗauki matakin da dokar UEFA ta tanada game da lamarin wariya.

Musanta zargi

An kuma ga ɗanwasan Real Madrid, Kylian Mbappe yana jan ragamar masu neman a ƙauracewa wasan matuƙar ba a ɗauki mataki ba.

Mbappe ya bayyana abin da ya gani a wasan, “Ɗanwasa mai lamba 25… ya ja wuyan rigarsa [don rufe bakinsa] kuma ya ce Vini biri ne sau biyar. Na ji hakan. Akwai ‘ƴanwasan Benfica ma da suka ji”.

A Laraban nan ne hukumar UEFA ta fitar da sanarwa mai cewa, "An naɗa mai saka-ido kan ladabi da ladabtarwa don ya binciki zarge-zargen halayyar wariya yayin wasan Zakarun Turai na UEFA Champions, kakar 2025/2026 tsakanin Benfica da Real Madrid CF ranar 17 ga Fabrairun 2026.

Sai dai gabanin wannan sanarwa Prestianni mai shekaru 19 ya wallafa saƙo a shafinsa na soshiyar midiya yana kausasa musanta zarge-zargen, yana iƙirarin cewa jami’an Real Madrid sun sauya zancen. Ya jaddada cewa an samu saɓanin harshe ne yayin cecekucensa a wasan.

Rumbun Labarai
Toni Kroos ya soki gasar ƙwallo ta Saudiyya game da raina tasirin Ronaldo
Victor Osimhen ya ci ƙwallo ta 200 a rayuwarsa ta wasa
Atletico Madrid ta ce ta cim ma yarjejeniya da Atalanta kan ɗanwasan gaban Nijeriya Ademola Lookman
Real Madrid za ta sake karawa da Benfica a wasan cike gurbi na Gasar Zakarun Turai
Mourinho ya bai wa Kocin Real Madrid haƙuri bayan Benfica ta doke Madrid a Gasar Zakarun Turai
CAF ta dakatar da kocin Senegal da Achraf Hakimi
Cole Palmer na son komawa Man United, Liverpool ba za ta rabu da kyaftin dinta, Virgil van Dijk ba
'Yanwasan Senegal sun samu kyautar kuɗi da fuloti saboda lashe Kofin AFCON
Dubban mutane sun halarci bikin karrama Zakarun Kofin AFCON a Senegal
Real Madrid ta sallami Xabi Alonso, ta nada Alvaro Arbeloa sabon koci
Hukumar CAF ta yi tir da rashin ɗa'a a zagayen kwata-fainal na AFCON 2025
Ɗan wasan Ghana Semenyo ya koma Man City daga Bournemouth kan dala miliyan 87
Yadda ƙarin kuɗaɗen tallafi ke taimaka wa mata ‘yanwasan ƙwallon ƙafa da ke fama da nakasa a Kenya
Wane ne Liam Rosenior, sabon kocin Chelsea?
Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim bayan ya soki shugabancin kungiyar
An sallami Anthony Joshua daga asibiti
Abubuwa 5 game da mai jiran Man United ta ci wasa 5 a jere, wanda ya kwana 452 ba aski
Yadda Tanzania ta tsallaka gaba da maki biyu kacal a gasar AFCON 2025
Hatsarin mota ya rutsa da Anthony Joshua a jihar Ogun ta Nijeriya
AFCON 2025: Za a fara wasannin ƙarshe na matakin rukuni don tantance ƙasashe 16 masu tsallakawa gaba