Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni

Tun da fari a sanarwar da ta fitar, Rundunar Tsaro ta Ghana, GAF ta ce mutum shida ne suka mutu a wajen jarabawar neman aikin da aka yi ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2025.

By
Mutum 12 sun mutu  a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni

Rahotanni daga Ghana sun ce mutum 12 sun rasa rayukansu sannan wasu da dama sun jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar daukar aiki ta sojoji a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin kasar.

Tun da fari a sanarwar da ta fitar, Rundunar Tsaro ta Ghana, GAF ta ce mutum shida ne suka mutu a wajen jarabawar neman aikin da aka yi ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2025.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6.20 na safe agogon kasar, a yayin da dumbin masu neman aikin suka take tsarin shiga wajen inda suka kutsa ba a cikin tsari ba, kafin lokacin fara jarabawar ya yi.

‎Sanarwar ta ce mutum shida sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata a turmutsutsun. A yanzu haka wadanda suka ji rauni na asibitin sojoji ana kula da su.

Amma rahotanni sun ce yawan wadanda suka mutun ya karu zuwa 12.

‎”Rundunar Tsaron Ghana tana bai wa al’umma tabbacin cewa tawagogin lafiya suna aiki ba gajiyawa don kula da wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar, tana mai cewa ana kuma shirye-shiryen sanar da iyalan wadanda suka rasu batun.

Rundunar TSaron Ghana ta mika sakon jaje da na ta’azziyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma fatan samun sauki ga marasa lafiya.