| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Sanarwar ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Rundunar 'yansandan ta ce ta zafafa ƙoƙarin kamo sauran waɗanda ke da alaƙ da harin

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen jihar Kano da ke arewacin ƙasar ta ce ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a mutuwar Ibrahim Khalil Danshagamu a unguwar Gaida ta Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Laraba ta ce ana gudanar da bincike kan batun kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

Sanarwa ta ce ranar 8 ga watan Satumba ne rundunar ta samu rahoto daga ‘yan sa-kai na unguwar Gaida cewa wasu ɓata-gari da ba a san su wane ne ba sun kutsa gidan mutumin inda suka kai masa hari da abubuwa masu tsini.

“Jami’an ofishin ‘yansandan na Kumbotso sun garzaya inda lamarin ya auku. Nan-take suka kai wanda lamarin ya shafa Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammad na Kano domin samun magani na gaggawa, inda wani likita ya tabbatar da cewa ya rasu a lokacin da ya isa,” in ji sanarwar.

Masu AlakaTRT Afrika - ‘Yansandan Nijeriya sun kama wani mutum kan zargin watsa wa matarsa fetur da cinna mata wuta

Sanarwar ta ƙara da cewa DPO na ofishin ‘yansandan Kumbotso da jami’ai daga rundunar ‘yansandan jihar sun yi aiki da masu ruwa da tsaki bisa umarnin kwamishin ‘yansandan jihar lamarin da ya sa suka kamo wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a mutuwarsa.

“A halin yanzu waɗanda ake zargin suna hannu inda ake musu tambayoyi,” in ji sanarwar. Kazalika sanarwar ta ce rundunar ta zafafa ƙoƙarin kamo duk wani mutum da ke alaƙa da laifin.

CSP Kiyawa ya ce ana karɓar bayanai kuma ana bin matakan bincike domin tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru da kuma dalilin da ya haddasa kai harin.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana damuwa sosai game da aukuwar lamarin tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, in ji sanarwar.

Kazalika sanarwa ta ambato kwamishinan yana cewa:“ Rundunar ‘yansandan jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a aikinta na kare rayuka da kadarori. Muna tabbatar wa mutanen Kano cewa za a bi hanyar tabbatar da adalci har zuwa ƙarshenta.”