Yaƙin da ake yi da ta'addancin Daesh yana ƙara ƙarfi: Erdogan
Shugaban Turkiyya ya ce kawar da ta'addancin 'yan a-aware da ke barazana ga arewacin Syria zai kawo sauƙi ga ɗaukacin yankin.
Yaƙin da ake yi da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh yana ƙara ƙarfi da karsashi, inda ake tumɓuke ainihin rushin ta’addanci daga yankin Gabas ta Tsakiya, a cewar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
“Da zarar an kawar da barazanar ta’addanci ta ‘yan a-aware daga arewacin Syria, ba al’ummar Syria ne kawai za su samu sauƙi ba, har da sauran al’ummar yankin," in ji Erdogan a ranar Asabar a wajen bikin miƙa sabbin gidaje da aka gina a lardin Aydin na ƙasar Turkiyya.
Ya jaddada buƙatar haɗa kai da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Syria yana mai cewa hakan zai amfani dukkan al’ummominta.
Ya ƙara da cewa, “waɗanda za su ci moriya idan aka haɗa kai da samar da zaman lafiya a Syria su ne Larabawa, Turkmaniyawa, Kurdawa, Alawiyawa, Druze, Kiristoci da dukkan al’ummar Syria.”.
Da yake magana kan harkokin duniya, Erdogan ya ce muhawarar da ake yi a wannan makon a wurin taron tattalin arzikin duniya na World Economic Forum a birnin Davos ya nuna cewa ƙasashen yammacin duniya suna goyon bayan daɗaɗɗen matsayin Turkiyya na sukar tsarin duniya na yanzu.