An gabatar da kudirin tsige mataimakin gwamnan Jihar Kano Aminu Abdussalam Gwarzo a ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini Dala ne ya tabbatar da yunƙurin batun gabatar da kudirin tsige mataimakin gwamnan.
Ya bayyana cewa an gabatar da kudirin tsige Gwarzon saboda zarge-zarge kusan guda huɗu waɗanda suka shafi amfani da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
“Ya cancanci idan ya zama mai laifi a kan waɗannan abubuwa, a tsige shi daga kujerarsa, kuma wannan ba za ta samu ba gabatar da wannan ɗin ma, sai an samu aƙalla ɗaya bisa uku na adadin ‘yan majalisa sun saka hannu a kan takardar a kawo wannan kudiri na sanar aikata irin wannan laifi,” in ji Lawal Hussaini Dala.
Ya bayyana cewa a halin yanzu majalisa ta amince a aika masa da takardar tuhuma inda aka ba shi mako biyu kan ya yi wa majalisa bayani domin kare kansa tun daga ranar da aka kai masa takarda.
A kwanakin baya ne dai gwamnan Kanoo Abba Kabir Yusuf ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC, inda mataimakin gwamnan jihar ya ƙi bin sa zuwa sabuwar jam’iyyar.
Wannan ne ya sa ake zargin aka yi ta samun takun saƙa tsakaninsa da maigidansa Abba Kabir Yusuf













