| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun tsaro sun ƙwace makamai a jihar Kogi ta Nijeriya tare da kama mutum uku
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa nasarar kama makaman wata alama ce cewa tana gaba da waɗanda ke neman barazana ga zaman lafiyar jihar.
Dakarun tsaro sun ƙwace makamai a jihar Kogi ta Nijeriya tare da kama mutum uku
TSOHON HOTO: Safarar miyagun makamai na cikin ababen da ke ruruta wutan rashin tsaro a sassan Nijeriya / Nigerian army

An kama wasu makamai da aka yi imanin cewa za a kai su ga ‘yanta’adda da ke neman yi wa zaman lafiya zagon ƙasa a jihar Kogi a tsakiyar Nijeriya ne a wani aikin tsaro na haɗin gwiwa.

Gwamnatin jihar ce ta bayyana wannan a wata sanarwar da kwamishinan watsa labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar ranar Litinin, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.

Ta bayyana cewa aikin kama makaman ya yi nasara ne sakamakon aiki tare tsakanin jami’an tsaro na cikin gundumomi a ƙarƙashin tsarin tsaron jihar Kogi da dakarun tsaro na musamman da ke aiki a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkar tsaro (ONSA), da kuma dakarun birged na 12 na sojin Nijeriya, inda suka yi aiki bisa bayanan sirri masu tushe.

Gwamnatin ta ce bayanai na farko-farko sun nuna cewa jami’an tsaro sun sami bayanan sirri game da tafiyar makamai da ake son kai wa masu aikata laifuka da ke aika-aika a yankin jihar Kogi.

Sanarwar ta ce bayanan sirrin sun nuna cewa ana amfani da wata mota samfurin Golf 2 domin safarar makaman.

“Yayin da suke ɗaukar mataki cikin gaggawa, hukumomin tsaro sun tsara matakai a faɗin kan iyakokin jihar, kuma bisa aiki da gwamnatin jihar Sokoto da hukumomin tsaro a jihar, sun bi sawun tafiyar waɗanda ake zargin tare da sa ido sosai kan harkokinsu.

“Aikin ya sa an kama waɗanda ake zargi uku a jihar Sokoto bayan an shafe makonni biyu ana sa ido a kansu a ɓoye . Bincike na farko farko sun ba da muhimman bayanan sirri, yayin da ƙoƙari ke tafe domin kama sauran ‘yan ƙungiyar da ke safarar miyagun makamai da ke neman ruruta wutar aikata laifuka a jihar Kogi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Yayain da suke ginawa a kan bayanan sirrin da suka samu sakamakon aikin, jami’an tsaro sun yi nasarar kama tarin makaman da aka yi niyyar kai wa masu aikata laifuka a jihar Kogi.

Motar samfurin Golf 2 da aka yi amfani da ita wajen safarar makaman daga baya an ƙwace ta a Kabba, a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu.

“Ababen da aka ƙwace a samamen sun haɗa da bindigogi biyu ƙirar AK-47 da wasu gidajen harsasai na AK-47, da harsasai saba’in da bakwai masu girman milimita 7.62 da ƙananan bindigogi biyu da harsasan ƙananan bindigogi sha biyu da kayayyakin soji da ake ganin ana son a yi amfani da shi ne domin amfanin masu aikata laifuka a aika-aikarsu,” a cewarsa.

Gwamnatin jihar ta kuma bayyana cewa rahotanni na bayanan sirri sun nuna cewa makaman da aka kama wani ɓangare ne na ƙoƙarin masu aikata laifukan na sake ƙara yawan makamansu da suka fara ƙarewa bayan sun samu komabaya na aiki a cikin ‘yan makonnin nan, “musamman biyo bayan kashe ƙasurgumin shugaban ‘yanbindiga, Kachalla Battijo, ranar 10 ga watan Yunin 2026, bayan ƙoƙarinsa na garkuwa da ɗaliban makarantar sakandaren gwamnati ta Iluke Bunu”.

Ta bayyana cewa, yayin da take tunanin yiwuwar hare-hare na ramuwar gayya da kuma ƙoƙarin yanke ƙauna na masu aikata laifuka da ke tserewa na sake haɗuwa da kuma sake samun makamai, nan take ta zafafa ƙoƙarin tattara bayanan sirrinta.