RSF ta Sudan ta kai hari da jirgi maras matuƙi, ta kashe gomman mutane da yara

Farmakin da RSF ta kai ya afku kusa da birnin Rahad a lardin Kordofan ta Arewa, a cewar Ƙungiyar Likitocin Sudan, wadda ke bibiyar rikicin da ake yi a ƙasar.

By
Harin RSF ya faru a kusa da birnin Rahad / AA

Wani hari da jirgin sama marar matuki da wata ƙungiyar RSF ta Sudan ta kai kan wata mota da ke ɗauke da iyalai ’yan gudun hijira a tsakiyar Sudan a ranar Asabar ya kashe aƙalla mutane 24, ciki har da yara takwas, in ji wata ƙungiyar likitoci.

Farmakin da RSF ta kai ya afku kusa da birnin Rahad a lardin Kordofan ta Arewa, a cewar Ƙungiyar Likitocin Sudan, wadda ke bibiyar rikicin da ake yi a ƙasar.

Motar tana ɗauke da mutanen da suka yi ƙaura daga gidajensu bayan ɓarkewar riki a yankin Dubeiker na Kordofan ta Arewa, in ji ƙungiyar likitocin a cikin wata sanarwa.

Daga cikin yaran da suka mutu akwai jarirai biyu, in ji ƙungiyar.

Karuwar mace-macen yara

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yara UNICEF a ranar Juma’a ta ce aƙalla yaran Sudan 20 ne suka mutu a watan Janairu, mafi yawansu a yankunan Kordofan da Darfur a yammacin Sudan.

A cikin rahoton da UNICEF ta wallafa kan halin da yara ke ciki a yankin, hukumar ta yi gargaɗin cewa “miliyoyin yara a Sudan na buƙatar taimakon rayuwa, kariya da dawo da muhimman ayyukan jama’a” yayin da rikici ke ci gaba da lalata manyan sassan ƙasar.

UNICEF ta ce an riga an tabbatar da akwai yunwa a Al Fasher da ke Darfur ta Arewa da kuma a Kadugli da ke Kordofan, sannan kimanin wasu wurare guda 20 na fuskantar haɗarin shiga cikin wannan yanayi.

Daga cikin jihohin Sudan guda 18, RSF na da iko da dukkanin jihohi biyar na yammacin yankin Darfur, sai dai wasu sassan Darfur ta Arewa har yanzu na ƙarƙshin sojojin ƙasar. Rundunar sojin Sudan na riƙe da mafi yawan yankunan sauran jihohin 13 a kudu, arewa, gabas da tsakiyar ƙasar, ciki har da babban birnin Khartoum.

Faɗan da ke tsakanin rundunar sojin Sudan da RSF ya fara ne a watan Afrilun 2023, sannan ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da mayar da miliyoyin mutane ’yan gudun hijira.