| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja
Tawaga daga ofishin NESREA reshen Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Kodinetan jihar, Hena Dangari Emmanuel, ta kai ziyara wurin domin tantance abin da ya faru tare da fara bincike.
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja

Hukumar Kula da Ka'idojin Muhalli ta Nijeriya (NESREA) ta fara gudanar da bincike kan zargin zubewar wani sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja, bayan da wata farar kumfa mai yawa ya bayyana a wurin.

Tawaga daga ofishin NESREA reshen Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Kodinetan jihar, Hena Dangari Emmanuel, ta kai ziyara wurin domin tantance abin da ya faru tare da fara bincike.

A yayin ziyarar, tawagar ta gana da Kwamandan 'Yansanda na Jere, ACP Sani Zubairu, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) na yankin, da kuma shugaban al'ummar yankin domin tattara bayanai kan lamarin.

Sakamakon binciken farko ya nuna cewa watai babban motar dakon kaya ce ta yi haɗari, lamarin da ya haddasa zubewar kayanta a wurin.

Tun da fari a makon da ya wuce ne wasu bidiyoyi da suka yaɗu a shafukan sada zumunta suka ja hankalin ‘yan Nijeriya, inda aka ga farin abin ya lulluɓe ƙasa, wasu suka dinga cewa gajimare ne ya faɗo wasu kuma suna cewa kumfa ce ke fitowa daga ƙasa.

A wani ɓangare na binciken, NESREA ta ce ta ɗauki samfurori na farar kumfar, ƙasa da kuma ruwan wani rafin da ke kusa da wurin domin a gwada su a dakin gwaje-gwaje.

Haka kuma, hukumar na ci gaba da tattara bayanai daga jami'an gwamnati da mazauna yankin domin gano haƙikanin abin da ya zube da kuma yiwuwar illarsa ga muhalli da lafiyar jama'a.

Hukumar ta shawarci jama'a da su guji taɓa farar kumfar, ƙasar da ke wurin da kuma ruwan rafin da ke kusa har sai an kammala binciken.

NESREA ta ce wannan matakin kariya ne domin kauce wa yiwuwar kamuwa da illa daga duk wani sinadari mai haɗari kafin sakamakon gwaje-gwajen dakin bincike ya fito.