Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi

Soyayya, rashi da kewa suna yin tasiri a kan Falasṭinawa a cikin yankin da aka rusa, a lokacin da suke azumtar wata mai tsarki na Ramadan yayin da ake ci gaba da fuskantar take yarjejeniyar tsagaita wuta daga Isra'ila.

By
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi / AP

Daga cikin abubuwan da matashi Bafalasɗine Amjad Joudeh ke tunawa masu daɗi na watan Ramadan akwai zuwa masallaci da yake shi da babansa da ɗan’uwansa don yin Sallar Tarawih a cikin watan Ramadan.

'Mukan tafi masallaci muna riƙe da hannun juna zuwa masallaci,' Amjad, mai shekaru 25, ya tuna da hakan a lokacin da yake zaune a gidansa da aka lalata wani ɓangarensa a arewacin birnin Gaza.

'Amma wannan shekara, zan tafi ni kaɗai,' Amjad, ɗan kasuwa, ya faɗa wa TRT World.

Ga sauran Falasdinawa a yankin Gaza da aka lalata, watan azumi na tuno wa mutane abin da suka rasa da kuma abin da ya rage na rayuwarsu bayan shekaru biyu na wani yaƙin kisan ƙare dangi wanda ya halaka fiye da mutum 70,000.

Falasdinawa a Gaza da sauran yankunan da aka mamaye na yin ibadu watan Ramadan a ƙarƙashin wata yarjeniyar tsagaita wuta mai rauni wadda Isra'ila ke ci gaba da ketawa kullum — tana kai mugayen farmakai ba ji ba gani da mamayar ‘yan-kama-wuri-zauna da kuma kashe fararen hula.

A lokutan nazari, Falasdinawa na tunawa da zamanin natsuwa na ibada tare a baya lokacin da masallatan Gaza ke cika a kowane dare don Tarawih — sallah ta musamman da ake yi kawai a watan azumi.

Yawancin waɗancan masallatai yanzu sun zama kufai, an ƙone su ko an rushe su bayan harin bama-bamai da aka kai a cikin shekara biyu da suka gabata.

Hare-haren jiragen sama da ake kai wa lokaci-lokaci da ke ci gaba da sanya tsoro a zuƙatan mutane ya sa an rage yin taron jama'a, ciki har da sallolin jam'i da ziyartar dangi, waɗanda a da suka kasance muhimman abubuwa da ake yi a wannan wata mai tsarki.

Amjad ya rasa dukan iyalinsa — iyaye da ƙannensa huɗu — a wani harin jirgin sama guda lokacin wannan yakin kisan ƙare dangi.

Abin da ya rage shi ne gidan da wani sashensa ya rushe da bangon da bam ya farfasa sai kewar da ke ruruwa a duk lokacin da Maghriba ta gabato a kowane yammaci.

'Ba abin da ke kewaye da ni a yanzu illa baƙin ciki. Ina ta tuna da yanzu fa iyalina suna nan muna azumin Ramadan tare. Ina ganin fuskokinsu a ko ina. Tuna hakan na da ciwo, amma suna tare da ni,' in ji shi.

A shekarun baya, Sallar Tarawih na zama lokaci na haɗin-kai. Suhoor da iftar lokaci ne na raha da hira da juna. A wannan shekarar, kusan bai damu ma da abin da zai ci ba.

'A yanzu ne na san ma'anar yi wa kaina abin buɗa-baki,' in ji shi.

'Mahaifiyata da 'yar'uwata sukan kammala haɗa abincin buɗa-baki awa ɗaya kafin faduwar rana. Mahaifina yana kunna rediyo don sauraron karatun Alƙur'ani. 'Yan’uwana suna ta musu kan wanda zai ɗauki farantin kanafeh,' in ji shi, yana nufin wani kayan zaƙi na gargajiya.

Mako 'na gaba' da ba zai taɓa zuwa ba

A cikin yanayin da ake ciki a Gaza, a tsakanin tantuna da gidaje da suka rushe, mutane na ƙoƙarin riƙe wasu ɓangarori na al'adun Ramadan domin yin ibada kamar yadda za su iya.

Ba koyaushe hakan ke aiki ba. Yawancin iyalai sun rasa wasu danginsu a lokacin wannan yakin kisan ƙare dangi. Duk da haka, suna ƙoƙari. Riƙe Ramadan kamar riƙe rai ne.

A bakin ƙofar wani tanti a kusa da bakin teku na birnin Gaza a zaune, Sanaa Al-Sharbase mai shekaru 41 ce tare da 'ya'yanta uku. Ta yi ƙoƙarin bayyana dalilin da ya sa wannan Ramadan ɗin ba zai yi kama da waɗanda suka gabata ba. Mijinta ya ji rauni sosai a lokacin yakin kuma ba ya iya aiki.

'Kafin haka yana samun dala 800 a wata,' ta faɗa wa TRT World. 'Yanzu yana samun dala 200 kacal a tallafin dayake samu a aikinsa.'

Iyalin na rayuwa ne da wannan ƙananan kuɗin da taimakon jinƙai wanda ba ya wadata wajen sayen abinci da magani sosai.

Wasu fitilun takarda da aka yi da hannu da aka rataye a jikin tantin suna kaɗawa. Su ne abubuwan da ke saka ta farin ciki da tuna mata ita da ‘ya;yanta cewa Ramadan ya iso.

'Kowane Ramadan, nakan sayi fitulun lantarki masu ado ko da ƙanana ne,' in ji ta. 'Nakan ƙawata gida. Ba masu yawa ba ne, amma suna sa yara farin ciki. Wannan shi ne Ramadan na farko da ban sayi kayan ado ba.'

Kayan ado yanzu sun fi tsada sau biyar fiye da da.

'Raina yana ƙunci idan suna tambaya, "Yaushe za mu sayi fitulun adon Ramadan?" Ba ni da amsa mai daɗi a gare su.'

Lokacin da 'ya'yanta suka nemi ta rataya fitilun a cikin tantin sai ta ce musu sai 'Mako mai zuwa.' Ta san dai sosai cewa makon ba zai zo ba.

A Gaza, yawancin iyalai suna da al'adar dafa miya mai ganye da ake kira molokhiya da kuma kaza a ranar farko ta Ramadan. Wannan shekara, Sanaa ba ta samu sararin yin haka ba.

'Ba zan iya sayen nama ba gabaɗaya,' in ji ta.

Yaranta watakila ba su fahimci wahalar tattalin arziki gaba ɗaya ba, amma suna jin rashin annashuwa. Ta yi ƙoƙarin maye gurbin ta dafa abinci ba tare da nama ba kuma ta tsawaita wasu ƙanana yankakken ƙirjin kaza yadda za su isa.

Mijinta yana zaune shiru a can cikin tantin. Raunin da ya samu ya hana shi iya magana. 'Raunin na masa zafi,' ta ce. 'Amma abin da ya fi masa zafi shi ne jin rashin ƙarfin da yake da shi.'

A farkon Ramadan, yana faranta ran yara da ba su abin da suka so.

Domin kare shi daga jin kunya, ta gaya wa yara cewa mahaifinsu 'shi ne mutumin ƙarfi a duniya' kuma zai koma aiki idan ya samu lafiya.

'Ramadan har yanzu wata ne na bayarwa,' ta ce. 'Muna da kyawawan tunani … ziyartar dangi da musayar abinci. Yanzu, kusan ba mu da isasshen cika farantin mu.'

Wa zai yi kayan zaƙi?

Ga Ihab Hassanein, mai shekaru 42, Ramadan ya dawo masa da ciwon tunanin matarsa, wadda ta rasu 'yan watanni da suka wuce, bayan fama da jinya.

A cikin shekaru goma sha biyar din da suka yi tare akwai abubuwa da dama na soyayya da ƙauna a lokutan Ramadan.

'Ba zan iya tunanin yin buda-baki ba tare da ita ba,' Ihab, injiniyan kwamfuta, ya faɗa wa TRT World a gidansa a tsakiyar Gaza.

'Ita ce ke zaɓar abincin. Ta nace mu kasance muna zaune kafin kiran sallah. Ta tsara rayuwarmu yadda ya kamata.'

Yaransa guda uku — masu shekaru 14, 12 da 9 — suna ci gaba da kin yarda.

'Suna guje wa furta 'mama ta rasu'. Ni ma haka nake.'

Ramadan na farko ba tare da ita ba ya sake buɗe tambayoyi marasa sauƙi.

'Shin mama na azumi tare da mu a lokacin Ramadan?' diyata mai shekara 12, Retal, ta tambaya. 'Eh,' na ce mata. 'Kuma tana cin (kayan zaki) qatayef a iftar.'

Yana jin tsoro lokacin da zai daga hannayensa shi kaɗai don yin addu'a a yamma. A da sukan yi addu'o'i tare.

'Zan zauna tare da 'ya'yana. Za mu karanta Al-Fatiha a gare ta a duk lokacin buɗe-baki da sahur. Zan ba su labarin Ramadan ɗinmu na farko tare da yadda muka yi dariya lokacin da ta sanya sukari maimakon gishiri a miya. Ba na so ta zama hoton bango kawai. Ina so tunaninta ya zauna a rayuwarmu.'

Wannan shekara, Ramadan a Gaza ba ya kama da abin da yake a da. Ya zo ne bayan wani yaki da ya tarwatsa tunani da yawa. Amma bai gushe daga zuciya gaba ɗaya ba.

Ga kowane iyali, Ramadan na ɗauke da ƙananan abubuwa masu zurfin rai da kewa da tunawa da baya.

Amjad na neman hanyar jure kadaicinsa. Sanaa tana yin fitilun maraba da Ramadan na takarda. Ihab ya kasa daina tunanin matarsa a lokuta na musamman na Ramadan.