| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Bankin Cigaban Afirka ya amince da fitar da dala miliyan 61 don tallafa wa mata a Nijeriya
Bankin Cigaban Afirka ya amince da fitar da dala miliyan 61 ga Bankin Cigaba na Nijeriya don habaka samun basussuka ga kasuwancin da mata ke yi a Nijeriya, musamman ma ayyukan noma da auran fannonin tattalin arziki da ba a tallafawa a kasar.
Bankin Cigaban Afirka ya amince da fitar da dala miliyan 61 don tallafa wa mata a Nijeriya
Bayar da tallafin zai mayar da hankali kan ayukan noma da sauran su. / Reuters

Sanarwar da bankin ya fitar ta ce, kudaden da bankin ya fitar sun hada da dala miliyan 50 na bashin da zai yi duba ga jinsi, dala miliyan 8 na manoma da kananan sana’o’i d akuma dala miliyan uku na bashin tallafin Tabbatarwa ga Mata a Afirka wanda Shirin Tallafawa Mata Masu Sana’o’i ke daukar nauyi.

Bankin na Cigaban Afirka ya kuma ce za a bayar da kudaden ta hannun cibiyoyin kudi da ke aiki da Bankin Cigaba na Nijeriya da kuma kanana da matsakaitan sana’o’in kasar.

An ware sama da kashi 95 na kudaden ga kasuwancin da mata ke yi da kasuwancn da mata ke jagoranta, wanda masu nazari suka bayyana a matsayin babban kokarin kawar da gibin samun kudade ga mata masu sana’o’i a kasa mafi yawan jama’a a Afirka.

Ana sa ran tallafin zai kuma karfafa kasuwancin noma da samar da abinci, bangarorin da aka dauka da muhimmanci a cigaban tattalin arzikin Nijeriya da samar da abinci.