Shugaban Amurka Donald Trump ya halarci taron karɓar gawawwakin sojojin Amurka huɗu da aka koma da su ƙasar cikin akwatunan gawa da aka lulluɓe da tutar Amurka a jihar Delaware, bayan an kashe su a hare-haren Iran a Gabas ta Tsakiya.
Taron, wanda ake kira "dignified transfer", ya gudana ne a ranar Laraba yayin da ake ci gaba da nuna rashin jin daɗi kan yaƙin da Amurka ke yi da Iran.
Ya zuwa yanzu yaƙin ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 37.5, da kuma ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka 18, sannan fiye da sojoji 450 sun jikkata.
Yaƙin ya kuma yi sanadin mutuwar dubban 'yan Iran.
'Yan majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyun Republican da Democrat sun fara bayyana damuwa kan yaƙin, wanda ya haddasa tashin farashin mai a duniya kuma babu alamun zai ƙare nan ba da jimawa ba.
Trump ya tafi Sansanin Sojin Sama na Dover da ke jihar Delaware domin halartar bikin.
"Za mu karrama su. Kuma wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi wahala a gare ni, amma dole ne a yi shi," in ji Trump kafin ya tafi bikin.
Shugabannin Amurka, mataimakan shugabanni da manyan jami'ai kan halarci irin wannan bikin na karɓar gawarwakin sojoji a Dover, inda wurin ke da mafi girman cibiyar adana gawawwakin sojoji a Amurka, musamman a lokacin yaƙi ko rikici da ke janyo mutuwar sojoji.
Harin sansanin Jordan
Sojojin Amurka uku da aka kashe lokacin da wani makami mai linzami na Iran ya sauka a barikin da suke kwance suna barci a Sansanin Sojin Sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan a ranar Jumma'a sun haɗa da Laftanar Tyler James Feehan mai shekaru 25, Sajan Angel S. Rampersad mai shekaru 28, da Soja Isabella Gonzales mai shekaru 19.
Dukkansu uku suna aiki ne a rundunonin kariyar sararin samaniyar sojojin Amurka.
Mutum na huɗu da ya mutu shi ne Sajan Michael Emmanuel Swinton mai shekaru 30, wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani lamari daban a Erbil na ƙasar Iraki yayin da ake gudanar da aikin tarwatsa wani jirgi maras matuƙi.
Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon a ranar Litinin ta ce sojoji 100 sun jikkata tun daga ranar 7 ga Yuli, kuma kashi 96 cikin 100 daga cikinsu sun koma bakin aiki.
Wani binciken jin ra'ayin jama'a da kamfanin Reuters/Ipsos ya gudanar a farkon wannan watan ya nuna cewa Amurkawa huɗu cikin biyar na ganin yaƙin Amurka da Iran zai ɗauki lokaci mai tsawo. Binciken ya kuma nuna cewa kashi 37 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun amince da hare-haren sojin Amurka kan Iran.
Rahoton ya kuma nuna cewa farin jinin Trump ya ƙara yin ƙasa sosai fiye da kowane lokaci a rayuwarsa ta siyasa tun bayan fara rikicin, yayin da masa dabarun siyasa na Jam'iyyar Republican ke gargaɗin cewa ƙarin tsadar rayuwa ta ƙara jawo jama’a ba su samun sauƙi duk da rage haraji da aka yi.
Hauhawar farashin man fetur da tsadar rayuwa na zama babbar barazana ga jam'iyyar Republican ta Trump gabanin zaɓen tsakiyar wa'adi na watan Nuwamba, inda jam'iyyar ke fuskantar yiwuwar rasa rinjayenta a Majalisar Wakilai, kuma watakila ma ta rasa ikon da take da shi a Majalisar Dattawa.












