| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Somaliya ta karɓi kayan aiki na zamani daga Turkiyya don inganta harkar noma
A ranar Lahadi ne kasar Somaliya ta karɓi kayan aiki na zamani daga Hukumar Ba da Tallafi da Daidaita Ayyuka ta Turkiyya (TİKA), domin ƙarfafawa da kuma zamantar da ayyukan Ma’aikatar Noma da Ban ruwa ta kasar.
Somaliya ta karɓi kayan aiki na zamani daga Turkiyya don inganta harkar noma
Lebanon ta yi maraba da yarjejeniyar, tana mai cewa ta amince da cewa kwanciyar hankali da tsaron kasar na da muhimmanci ga kowane sulhu mai dorewa a yankin.

Tallafin na kasar Turkiyya zai inganta yadda ma’aikatar ke gudanar da ayyukanta, ya kuma gaggauta isar da ayyuka ga al’umma, tare da taimaka wa Somaliya wajen cimma burin dogaro da kai a fannin abinci, kamar yadda Ministan Noma da Ban ruwa na Somaliya, Mohamed Abdi Hayir Mareye, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

“Ina son miƙa godiyata ta musamman ga hukumar TİKA, hukumar raya ƙasa ta ’yan uwanmu na Jamhuriyar Turkiyya, bisa isar da kashi na farko na tallafin da suka yi alkawari,” inji ministan bayan taron miƙa kayan aikin a babban birnin kasar, Mogadishu.

Ya kuma bayyana cewa, an gabatar da wannan buƙatar ne ga Shugaban hukumar TİKA, Abdullahi Eren, a wani taro da aka gudanar a Ankara a shekarar 2025.

‘Muna daraja wannan haɗin gwiwa sosai’

Kayan aikin da aka miƙa sun haɗa da kwamfutoci, na’urorin buga takardu da kuma allunan talabijin (TV screens).

“Muna daraja wannan haɗin gwiwa sosai kuma muna fatan ci gaba da yin aiki tare da abokanmu na ƙasar Turkiyya,” in ji ministan.

Dangantaka tsakanin Somaliya da Turkiyya ta ƙara ƙarfi ne tun a shekarar 2011, bayan ziyarar da Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (wanda a wancan lokacin shi ne Firayim Minista) ya kai ƙasar.

Tun daga wancan lokacin, tallafin jin kai da na fasaha da Turkiyya ta bai wa Somaliya ya wuce dalar Amurka biliyan 1, wanda ya haɗa da ayyuka a fannonin lafiya, ilimi, ayyukan kananan hukumomi, da kuma ababen more rayuwa.