Jite Odeworitse: Attajirin Nijeriya ya janyo ce-ce-ku-ce sakamakon auren mata 19
Jite Tesigimoje ya ce yana ganin auren mace fiye da ɗaya ya fi yaudarar 'yan mata da dama
Jite Odeworitse: Attajirin Nijeriya ya janyo ce-ce-ku-ce sakamakon auren mata 19
Attajirin mai harkar mai Jite Odeworitse Tesigimoje, ɗan Jihar Delta yana da ra'ayin a ringa auren mace fiye da ɗaya, sai dai ra'ayin nasa ya janyo ce-ce-ku-ce.
9 Oktoba 2025

Hamshakin attajirin nan na Nijeriya, Jite Odeworitse Tesigimoje, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya auri matarsa ​​ta 19 a wani biki mai ƙayatarwa.

Attajirin mai shekaru 43 daga jihar Delta mai arzikin man fetur, fitaccen dan kasuwa ne kuma yana yawan kiran a ringa aurar mace fiye da ɗaya. Hotunan bikin aurensa na baya-bayan nan sun yi ta yawo cikin sauri, inda suka haifar da mahawar game da al'adu, da soyayyar zamani.

A wata hira da jaridar The Nation ta Nijeriya, hamshakin mai harkar man fetur ya zayyana falsafarsa, inda ya bayyana zabin aurensa a matsayin sukar ka’idojin ƙasashen yamma kai-tsaye.

Ya ce, “‘Yan mulkin mallaka sun ce mana auren mace ɗaya ne hanya mafi kyau ta rayuwa. Amma kullum suna cikin aikata abin kunya. Me ya sa suke aikata abin da bai dace ba? Me ya sa suka yi mana ƙarya?

Ya ƙara da cewa auren mace fiye da daya ya fi a yaudari mata da yawa a wajen aure.

Attajirin ya ci gaba da bayyana cewa, gidan sa na nuni ne da bambancin ra’ayi da hadin kan Nijeriya, domin ya auri mata daga cikin manyan kabilun kasar da suka hada da Ibo, Yarbawa, Fulani da kuma kabilarsa ta Itsekiri.

'Auren jituwa'

Ko da yake yana son auren mace fiye da ɗaya, Tesigimoje ya yarda cewa ba kowa ne ya cancanci auren mace fiye da ɗaya ba, yana mai cewa yana bukatar “kuɗi mai yawa da kuma hankali.”

Da yake bayyana girman tanadin nasa, hamshakin attajirin ya ce matansa a birnin Lagos na Nijeriya kowacce tana zaune a gida mai ɗaki biyar kuma yana ba su alawus mai tsoka.

Sirrin jituwa, in ji shi, shi ne cikakken adalci. Tesigimoje ya ce, “Da zarar na yi wa mace ɗaya wani abu, dole ne na yi wa sauran ma.”

Mai harkar man ya jaddada cewa wannan daidaiton yana tabbatar da zaman lafiya a gidansa. Ya kuma yi nuni da cewa zai auri mata ta 20.

Duk da cewa auren mace fiye da ɗaya ya zama ruwan dare a Afirka, amma ba kasafai maza suke auren mata da yawa ba kamar yadda Tesigimoje ya yi. Sai dai ba a san adadin ‘ya’yansa ba.

Sai dai masu sharhi da dama sun soki zaɓin nasa, suna masu cewa hakan na ƙara ƙarfafa matsalolin da al’umma ke shiga, abin da kuma zai iya kawo cikas ga bunƙasar tattalin arzikin al'umma.

Rumbun Labarai
Yadda dafa abinci na haɗin gwiwa a Somaliya ke ciyar da ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsu
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihi
Amaren Gaza: Matan da yaƙin Isra’ila ya mayar zawarawa rabi da rabi
Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Hijirar tsuntsaye: Afrika na tattaro kan duniya wajen ceto muhimman fadamu don biliyoyin tsuntsaye
Tsutsar Mopane: Daddaɗan abincin Namibia da ake ci tsawon zamanai
Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Dalilan da suka sa ake buƙatar mutane su samu abokai na zahiri a yayin da intanet ke jawo kaɗaitaka
Nairobi Birdman: Matashin da ke abota da tsuntsaye a Kenya
Yadda birai suka addabi wani gari a Afirka ta Kudu da "sata da ƙwace"
Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniya
Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Waiwaye kan tarihin Aikin Hajjin Annabta da yadda ake gudanar da shi