| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Kwalara ta kashe mutum 23 a Sudan, fiye da 310 sun kamu da cutar
Ƙungiyar Dar Hamar Emergency Room ta koka kan yadda ƙarancin abinci ke tilasta wa mazauna yankin Kordofan ta Yamma amfani da abincin dabbobi domin ciyar da ’ya’yansu.
Kwalara ta kashe mutum 23 a Sudan, fiye da 310 sun kamu da cutar
Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin lafiya da ƙungiyoyin agaji da su gaggauta samar da kayan aikin jinya da magunguna

 Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da aka samu fiye da mutane 310 da suka kamu da cutar kwalara ko kuma ake zargin sun kamu da ita a yankuna biyu na Kordofan ta Yamma da ke kudancin Sudan, kamar yadda wata ƙungiyar agaji ta yankin ta bayyana a ranar Lahadi.

Ƙungiyar Dar Hamar Emergency Room, wadda ƙungiyar agaji ce da al'umma ke tafiyar da ita, ta yi gargaɗi a cikin wasu jerin sanarwa biyu da ta fitar kan taɓarɓarewar yanayin lafiya da na jinƙai a ƙauyen Humeir da Hilla Hussein da ke Ƙaramar Hukumar Al-Udayyah.

Ƙungiyar ta ce Humeir na fuskantar “mummunan yanayin lafiya,” inda aka kwantar da mutane 120 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a wata cibiyar killace masu cutar, yayin da aka samu mutuwar mutane 11.

Ta ce cibiyar killace masu cutar ba ta da isasshen ruwan allura da magungunan ceton rai, a daidai lokacin da adadin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ke ci gaba da ƙaruwa.

Ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin lafiya da ƙungiyoyin agaji da su gaggauta samar da kayan aikin jinya da magunguna, tana mai gargadin cewa yanayin na iya ƙara taɓarɓarewa.

A wata sanarwa ta daban, ƙungiyar ta ce rikicin lafiya da na jinƙai ya ƙara ta'azzara a Hilla Hussein, inda aka samu fiye da mutane 190 da suka kamu da cutar kwalara, yayin da mutane 12 suka mutu sakamakon cutar.

Ta ƙara da cewa matsalolin sufuri sun ware yankin, lamarin da ya sa aka samu matsala wajen fitar da marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali domin kai su asibiti don samun magani.

Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗi kan ƙara ta'azzarar matsalar ƙarancin abinci, inda ta ce yanayin ya tilasta wa wasu mazauna yankin amfani da abincin dabbobi domin ciyar da ’ya’yansu.

Ta yi kira ga ƙungiyoyin agaji da su gaggauta samar da magunguna da tallafin abinci ga mazauna yankin.

Ƙungiyar ba ta bayyana lokacin da aka samu mutuwar, tabbatar da kamuwa da cutar da kuma waɗanda ake zargin sun kamu da ita a yankunan biyu ba.

A ranar 14 ga Yuli, Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da daidaita ayyukan jin ƙai (OCHA) ya yi gargaɗin cewa ci gaba da yaƙe-yaƙe da barkewar cututtuka na jefa fararen-hula a faɗin Sudan cikin mawuyacin hali.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar 7 ga Yuli ta bayyana cewa an tabbatar da mutane 1,330 da suka kamu da cutar kwalara, yayin da mutane 114 suka mutu sakamakon barkewar cutar a Sudan.

Sudan na fama da rikici tsakanin sojojin ƙasar da rundunar Rapid Support Forces (RSF) tun daga watan Afrilun 2023, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba kusan mutane miliyan 13 da muhallansu, a cewar ƙididdigar Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ƙasa da ƙasa.