Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta shirya domin fuskantar harin ƙasa na Amurka, inda ya yi amfani da salon magana na rashin tsoro yayin da rikicinsu da Washington da Isra’ila ke ƙamari.
Da aka tambaye shi a wata hira ta bidiyo da kafar NBC News ranar Alhamis kan ko yana tsoron yiwuwar kutsawar Amurka, Araghchi ya ce a shirye Iran take.
“A’a, muna jiran su,” in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa Tehran na da yaƙinin cewa za ta iya arangama da dakarun Amurka kuma irin wannan matakin zai zama “babban bala’i ” ga Washington.
Kalaman na zuwa ne bayan hare-haren Amurka da Isra’ila da aka fara ranar 28 ga watan Fabrairu, hare-haren da hukumomin Iran suka ce sun kashe jagoran addini Ali Khamenei da wasu manyan jami’an tsaro.
Iran ta yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta
Duk da cewa rikicin na faɗaɗa, Araghchi ya ce Iran ba ta nemi tsagaita wuta ba.
Ya yi ishara ga yaƙi na ƙanƙanin lokaci da Isra’ila a shekarar da ta gabata, yana mai cewa Tehran ba ta nemi sulhu ba a wancan lokacin ma.
“A lokacin da ya gabata, Isra’ila ce ta nemi a tsagaita wuta,” in ji shi, inda yake ishara ga rikicin kwanaki 12 inda dakarun Isra’ila da na Amurka suka kai hare-haren kan tashoshin nukiliyar Iran.

Araghchi ya ce abin da Iran ta saka a gaba a rikicin da ake yi yanzu shi ne kawai ƙin amincewa da abin da ya bayyana a matsayin matakan da suka saɓa wa doka da aka ɗauka kan ƙasar.
“Babu mai nasara a wannan yaƙin,” in ji shi. “Nasararmu ita ce mu iya nuna ƙin amincewa.”
Musu game da hari mai muni da aka kai kan makaranta
Ministan na Iran ya kuma ɗora wa Amurka da Isra’ila alhakin kai hari a wata makarantar firamare a birnin Minab da ke kudancin Iran wanda ya ce ya kashe yara mata ‘yan makaranta 171 .
Araghchi ya ce jami’an sojin Iran su yi imanin cewa ɗaya daga cikin ƙasashen biyu ne kawai za su iya kai harin.
Jami’an Amurka sun musanta kai harin.
Pete Hegseth, sakataren tsaron Amurka, ya ce Washington tana bincike kan lamarin kuma ya jaddada cewa Amurka ba ta kai hari kan fararen-hula.
“Muna dubawa kuma muna bincike a kansa,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Mai magana da yawun Fadar White House Karoline Leavitt ma ta yi watsi da zargin, tana mai cewa Amurka ba ta kai hare-hare kan fararen-hula.
An dakatar da tattaunawa da Washington
Araghchi ya ce a halin yanzu Iran ba ta tuntuɓar masu shiga tsakanin na Amurka, ciki har da jakada Steve Witkoff ko kuma Jared Kushner.
Ya ce Iran ba ta da cikakkiyar hujjar sake fara tattaunawa bayan hare-haren soji suka biyo bayan matakan diflomasiyya na baya.
“Gaskiyar ita ce ba mu da wani abu mai kyau da za mu iya cewa game da tattaunawa da Amurka ba,” in ji Araghchi, yana mai zargin Washington da gaza tattaunawa da kyakkyawar niyya.
Duk da haka, ministan harkokin wajen Iran ya amince da cewa rikicin ka iya gaza fitar da wani sakamako ƙarara ga ko wanne daga cikin ɓangarorin biyu.
“Babu mai nasara a wannan yaƙin,” in ji shi.

















