Duk bayan ‘yan makonni, jiragen sama na dakon kaya da ake bai wa matuƙar tsaro sukan tashi daga Amurka ɗauke da katan-katan na banduran dalar Amurka ‘yan ɗari-ɗari, inda ake safararsu zuwa Babban Bankin Iraƙi a Baghdad.
Amma yanzu Amurka ta dakatar da wannan, tana bayyana cewa dalilin shi ne 'gazawar Iraƙi wajen hana hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanbindiga da Iran ke tallafawa suke kai wa cibiyoyin Amurka a Iraƙi da ƙasashe maƙwabta'.
Washington ta ce dakatar da jigilar dalar Amurka da kuma dakatar da shirye-shiryen haɗin-gwiwar tsaro da sojojin Iraƙi wani yunƙuri ne na tarwatsa “ƙungiyoyin ‘yanbindiga da Iran ke tallafawa”, a cewar rahoton Wall Street Journal ranar Talata.
An ce wannan shi ne karo na biyu da Amurka ta jingine shirin aika dala babban bankin Iraƙi tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya fara a ranar 28 ga Fabrairu, inda Tehran take ramawa da kai hare-hare kan Isra'ila, da kuma hari kan ƙasashen Gulf da ke masaukin kadarorin soja da na kuɗi na Amurka.
Wasu ƙungiyoyin masu ɗauke makamai a Iraƙi sun ce su ne ke kai hare-hare na kullum kan 'sansanonin abokan gaba' a cikin ƙasar da yankin gabaɗaya, amma daga baya sun dakatar da ayyukansu bayan sanarwar tsagaitawar wuta tsakanin Amurka da Iran.
'Gazawar gwamnatin Iraƙi wajen hana waɗannan hare-haren, yayin da wasu ɓangarorin da ake danganta su da gwamnatin Iraƙi ke ci gaba da ba wa ƙungiyoyin da Iran ke tallafawa kariya ta siyasa, ta kuɗi da ta aiki, wanda ke cutar da dangantakar Amurka da Iraƙi,' in ji mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott.
Yaushe Amurka ta fara tura daloli Iraƙi?
Wannan al'ada, wadda ta samo asali bayan mamayar da Amurka ta yi wa Iraƙi a 2003, tana ci gaba har yau, domin Iraƙi na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi dogaro da dalar Amurka a duniya.
Kuɗaɗen sayar da mai, waɗanda ke samar da kusan kashi 90–95 cikin ɗari na kasafin gwamnatin Iraƙi, ana biyan su ne da dalar Amurka kuma ana ajiye su a asusan Babban Bankin Amurka na New York.
Idan Baghdad na buƙatar tsabar kuɗi don biyan albashi, fansho, shigo da kaya, da kuma musayar kuɗi don tallafawa dinar na Iraƙi, ana tura takardun kuɗin dala na zahiri ta jirgin sama.
Tun bayan mamayar 2003, Amurka ta riƙe iko na zahiri kan kuɗaɗen shiga daga sayar da mai na Iraƙi, abin da ya ba Washington babbar dama da tasiri kan harkokin gwamnatin Baghdad.
Ta yaya Amurka ke sarrafa kuɗaɗen mai na Iraƙi?
Ikon Amurka kan kuɗaɗen shiga daga mai na Iraƙi ya samo asali ne musamman daga sarrafa kuɗaɗen mai ta hannun Bankin Federal Reserve na New York.
Bayan mamayar 2003, hukumar Coalition Provisional Authority (CPA), wadda Amurka ke jagoranta, ta kafa asusun Development Fund for Iraq (DFI), wanda aka ajiye a New York Fed.
Shugaba Amurka na lokacin, George Bush, ya sa hannu kan wata oda ta zartarwa, wadda tun daga nan duk shugabanni da suak gaje shi suke sabuntawa, kuma hakan ne ya kafa wannan tsari.
A ƙarshe, asusun DFI ya koma asusun Babban Bankin Iraƙi a Bankin Federal Reserve na New York.
Musayar daloli
Amurka ta janye sojojinta masu yaƙi daga Iraƙi a Disamban 2011, amma ta bar rundunar sojoji 2,500 don abin da Washington ke kira 'horarwa da ba da shawara ga rundunonin Iraƙi'.
Lokacin da gwamnatin Iraƙi ta nemi sojojin Amurka su bar ƙasar a 2020, an ruwaito cewa Washington ta yi barazanar yanke damar Iraƙi kan kuɗaɗen Bankin Federal Reserve na New York, inda Baghdad a ƙarshe ta ja da baya, in ji Reuters.
A tarihi, Iraƙi ta yi amfani da musayar daloli, wanda a hukumance ake kira 'foreign currency window', a matsayin babbar hanyar samar da daloli.
Bankuna masu zaman kansu da shagunan musayar kuɗi na iya yin tayin a kullum don sayen dalar Amurka ta amfani da dinar na Iraƙi.
Iraƙi ta kawo ƙarshen tsarin musayar a hukumance a farkon 2025, bayan matsi mai ƙarfi daga Amurka, a wani yunƙuri na kakkaɓe zargin tura daloli zuwa cibiyoyin da aka sanya wa takunkumi, musamman dai Iran.
















