Fitaccen malamin addinin Kirista a Nijeriya, Dolapo Lawal ya nemi afuwa ga magoya bayan Arsenal bayan ya yi abin da masu sharhi da dama suka kira “saƙon wahayi na ƙarya” game da kulob din.
Wannan ya zo ne bayan kulob ɗin na ƙwallon ƙafa da ke birnin London ya lashe kofin Premier League na Ingila karo na farko a cikin shekaru 22.
To, me ya sa faston na Nijeriya ya tsunduma cikin ce-ce-ku-ce kan ƙwallon ƙafa?
A watan Afrilu 2026, wani bidiyo na Fasto Dolapo Lawal na Zoe Household Global Church yana wa'azi ya janyo babban ce-ce-ku-ce.
Ba wa'azin addini kansa ne matsala ba. A tsakiyar hudubarsa, ya sauya magana ya fara yin nazarin ƙwallon ƙafa. Kuma ba wai huɗuba ta yin addu’a ga kulob ɗin ba.
Ya yi hasashe da izza cewa Arsenal ba za ta ci kofin Premier League ba a wannan kakar..
“Magoya bayan Arsenal 'yan asara ne”
Haka kuma ya shawarci mata kada su yi soyayya da masu goyon bayan Arsenal saboda ya ce su 'yan asara ne.
Fushin magoya bayan Arsenal a Nijeriya ya yi tsauri sosai a kafafen sada zumunta. Wannan ba abin mamaki ba ne.
Magoya bayan Arsenal a Nijeriya suna da sha'awa kuma suna da aminci ga kulob din. Sun yi ta sukarsa daga kowane bangare, suna cewa ya “la’anci” kulob ɗin.
Fasto Dolapo ya yi wani sabon bidiyo don kare kansa da neman afuwa. Kuma a nan ne sabon salo ya bayyana.
Ya bayyana cewa shi masoyin Manchester United ne kuma duk abin kawai “barkwancin ƙwallon kafa” ne, ba “saƙon wahayi” kamar yadda aka ruwaito ba.
Arsenal sun lashe kofin Premier League na Ingila, sabanin hasashen Fasto na Dolapo.
Sai ya ce, “To, kun nuna cewa na yi kuskure,” sannan ya ta ya magoya bayan Arsenal murna.
Amma hakan bai rage suka ba; wasu sun yi masa dariya suna cewa kawai ya na “borin kunya ne”.
Arsenal na ɗaya daga cikin kulob-kulob mafi shahara na Turai a Afirka, da miliyoyin magoya baya a fadin nahiyar da ke kallon wasanninsu a talabijin.
Bayan sun kammala a matsayi na biyu a cikin shekaru uku da suka gabata, Gunners sun samu kofin Ingila na farko tun lokacin 'Invincibles' na Arsène Wenger a 2004.
Kungiyar Mikel Arteta ta mamaye gasar a wannan kakar kuma an tabbatar sun zama zakaru bayan Manchester City ta yi kunnen doki 1-1 da Bournemouth a ranar Talata.
Wannan rikici a Nijeriya ya sake tayar da muhawara game da saƙon wahayi daga wasu fastoci da yadda ƙwallon ƙafa ta zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum a ƙasar da ke Yammacin Afirka da ma sauran wurare.


















