Hukumar ICPC ta ce za ta binciki shugaban NMDPRA Farouk Ahmed kan ƙorafin Dangote

A takardar ƙorafin da aka gabatar a ranar 16 ga Disamba, Dangote ya nemi a kama Ahmed, a gudanar da bincike tare da gurfanar da  Farouk  Farouk Ahmed a kotu kan zargin yin rayuwar ƙarya da kuɗin da yake samu a matsayin ma'aikacin gwamnati.

By
Aliko Dangote ya ce yana son a binciki shugaban hukumar NMDPRA / Reuters

Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta ce za ta yi bincike kan zargin da attajirin Afirka Aliko Dangote ya yi wa shugaban Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, Farouk Ahmed, kan zarginsa da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiya.

A cikin takardar ƙorafin da aka gabatar a ranar 16 ga Disamba, Dangote ya nemi a kama Ahmed, a gudanar da bincike tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya bisa zarginsa da yin rayuwar ƙarya da facaka da kuɗin da yake samu a matsayin ma'aikacin gwamnati.

‘Yan sa’o’i bayan attaijirin ya ɗauki wannan matakin ne hukumar ICPC ta bayyana cewa ta karɓi koken kuma ta yi alƙawarin bincike kan lamarin. 

“Hukuma mai zaman kanta da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC tana so ta tabbatar da cewa ta karɓi takardar koke a hukumance a yau Talata 16 ga watan Disambar shekarar 2025 daga Alhaji Aliko Dangote ta hanyar lauyansa,” kamar yadda mai magana da yawun hukumar, John Odey, ya rubuta a wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumuntan hukumar. 

“An rubuta takardar ƙorafin ce a kan shugaban hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed. Hukumar ICPC tana son ta bayyana cewa za a yi bincike kan ƙorafin yadda ya kamata.”

A cikin takardar ƙorafin da ya miƙa wa hukumar ICPC, attajirin ɗan asalin Jihar Kano, ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja (SAN), ya yi zargin cewa shugaban hukumar NMDPRA ya kashe, ba tare da hujjar hanyar samun kuɗi ta halal ba, kuɗi da ya kai dala miliyan bakwai kan karatun ‘ya’yansa huɗu a makarantun ƙasar Switzerland na tsawon shekaru shida.

Ya yi zargin cewa Ahmed ya yi amfani da hukumar NMDPRA domin satar kuɗi da kuma juya akalar kuɗin al’umma zuwa amfaninsa da kuma neman cim ma muradun kansa ta hanyar da ta saɓa wa muradun ‘yan Nijeriya.

"Babu shakka gaskiyar da ke sama game da cin amanar ofis, karya Dokar Ɗa'a ga jami'an gwamnati, azurta kai daga cin hanci da rashawa, da almubazzaranci babban laifi ne na cin hanci da rashawa wanda Hukumarku (ICPC) ta ba da iko bisa doka a ƙarƙashin sashe na 19, na Dokar ICPC don bincike da gurfanarwa," in ji Dangote.

"Bayan nasarar gurfanar da irin wannan mutumin, a ƙarƙashin sashe na 19 na Dokar ICPC, mutumin zai fuskanci ɗaurin shekaru biyar ba tare da zaɓin tara ba.

"Muna da ƙarfin hali mu bayyana cewa ICPC tana da matsayi mai kyau tare da hukumomi 'yan’uwanta don gurfanar da laifukan kuɗi da sauran laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa, kuma bayan kafa shari'ar farko, Kotuna ba sa jinkirin hukunta masu laifi.

Dangote ya yi alƙawarin gabatar da hujjoji don tabbatar da zarginsa na wadaƙar da Ahmed ke yi da azurta kansa da cin amanar aikinsa.

Majalisar wakilan Nijeriya dai ta gayyaci ɓangarorin biyu tana mai kira a gare su cewa su daina tone-tone a bainar jama’a.

‘Yanmajalisar sun ce rikicin ya saɓa wa ci-gaban da ake samu a fannin man fetur.

Alhaji Farouk Ahmed ya ƙaryata wata sanarwa da ke jawo a shafukan intanet cewa ya fitar da martani ga zargin aikata ba daidai ba da Dangote ya yi masa, yana mai kira a bar hukumar ICPC ta gudanar da aikinta tun da an miƙa mata ƙorafi a kansa.