| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Zanga-zanga ta ɓarke a Afirka Ta Kudu kan naɗin Sarkin 'yan ƙabilar Igbo
An naɗa shugaban ‘yan ƙabilar Igbo ‘yan Nijeriya Solomon Ogbonna Eziko a matsayin “Igwe Ndigbo” ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2026, lamarin da hukumomi a Eastern Cape ke ganin raini ne ga al’adun yankin da kuma ‘yancin kai.
Zanga-zanga ta ɓarke a Afirka Ta Kudu kan naɗin Sarkin 'yan ƙabilar Igbo
An naɗa ɗan Nijeriya Solomon Ogbonna Eziko a matsayin basarekn gargajiya na ƙabilar Igbo a Afirka ta Kudu ranar 24 ga watan Maris , 2026. / User Upload
20 awanni baya

Rikici ya ɓarke a lardin Eastern Cape na Afirka ta Kudu bayan wani naɗin sarauta na wani basaraken ƙabilar Igbo mai cike da ce-ce-ku-ce, inda masu zanga-zanga suka ƙona motoci da kuma fasa shagunan ‘yan Nijeriya.

An naɗa shugaban ‘yan ƙabilar Igbo ‘yan Nijeriya Solomon Ogbonna Eziko a matsayin “Igwe Ndigbo” ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2026, lamarin da hukumomi a Eastern Cape ke ganin raini ne ga al’adun yankin da kuma ‘yancin kai.

Jerin zanga-zangar, da aka yi a ƙarƙashin jagorancin ‘yan ƙungiyar ActionSA da shugabannin gargajiya da kuma mazauna yankin ranar Litinin, an fara yin su ne domin nuna rashin amincewa da abin da waɗanda suka shirya su suka kira take ‘yancin lardin da tsarin mulki da kuma tsarin masarautun gargajiyar da aka yarda da su.

Sai dai kuma, tashin hankali ya yi ƙamari cikin sauri a birnin KuGompo, inda jerin zanga-zangar suka rikiɗe zuwa rikici, lamarin da ya tilasta wa ‘yansanda shiga tsakani da kuma tarwatsa gungun mutanen, in ji kafar watsa labaran ƙasar SABC News.


Wasu bidiyoyi da aka wallafa a shafin X sun nuna masu zanga-zanga suna ƙona motoci da gine-gine da aka yi iƙirarin cewa na ‘yan ƙasashen waje ne yayin da dakarun tsaro ke ƙoƙarin dawo da doka da oda.

“Masu zanga-zanga sun ƙona motoci da gine-gine da aka yi iƙirarin cewa na ‘yan ƙasashen waje ne domin nuna rashin amincewarsu da naɗa wani basaraken Nijeriya a Eastern Cape,” kamar yadda Newsroom Afrika ta ruwaito.


Kazalika, CDR ta bayyana cewa rikicin ya nuna ƙarin taƙaicin da ake samu game da naɗin sarautar, inda ƙadarori na ‘yan ƙasashen ƙetare suka zama ababen da ake kai ma farmaƙi.
Lamarin dai ya ƙara taɓarɓarewa , inda kafar eNCA ke ba da rahoton cewa rikicin ya zama na salwantar da rayuka bayan an daɓa wuka wa wasu masu shaguna ‘yan ƙasar Ethiopia .

An kai aƙalla mutum biyu asibiti domin jinya yayin da aka lalata wasu motoci a cikin rikicin.

Shawara ga ‘yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin mai taken “Shawara ga dukkan ‘yan Nijeriya mazauna Jamhuriyar Afirka ta Kudu,” ofishin jakadancin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su yi taka-tsantsan yayin “tashin hankali” a ƙasar.

Ofishin jakadancin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su mayar da hankali kan tsaro a ko wane lokaci, su daidaita kai-komonsu da kuma taƙaita tattaunawa da waɗanda ba su sani ba.

Ya kuma shawarci ‘yan ƙasar su yi rage gudanar da harkokinsu, su ci gaba da bin doka tare da martaba dokoki da al’adun ƙasar.

An ƙara yi wa ‘yan ƙasar gargaɗin cewa su ƙaurace wa zanga-zanga ko kuma jerin gwanon ƙin jinin zanga-zanga da kuma ƙaurace wa nuna arziki da bai zama dole ba.

Shawarar ta kuma nemi ‘yan Nijeriya su gabatar da rahoton duk wata barazana ga rayuwa ko kadara ga hukumomi.

“Duk ‘yan ƙasa su nemi shawarar ofishin jakadanci a Pretoria ko kuma ƙaramin ofishin jakadanci a Johannesburg domin ƙarin bayani game da matakan tsaro idan da buƙatar yin hakan,” in ji sanarwar.