Kenya da Habasha suna daga cikin manyan ƙasashe a duniya da ke noman furanni wadanda ke samun yanayi mai kyau da kuma hasken rana a duk shekara.
Kenya na a matsayin ƙasa ta hudu a duniya da ke fitar da furanni, inda take samun fiye da dala 500 a kowace shekara kana tana da gonaki sama da 127, bayan ƙasar sai Netherlands, da Colombia, da kuma Ecuador.
Haka kuma ita ma Habasha babbar kasa wacce ke tasowa wajen noman furanni kuma ita ce ta biyu mafi girma a Afirka wajen fitar da shi, inda kasashen biyun suka mayar da hankali wajen samar da furannin wardi ga kasuwannin Turai.
Kenya tana samar da kusan kashi 40% na furannin da ake shigowa da su Turai kuma tana samar da kashi 15% na cinikayyarsa a duniya, wanda ke samun tallafi daga hanyoyin jiragen sama, gami da wadanda kamfanin jirgin saman kasarta, Kenya Airways ke fitarwa.
Masana a fannin noman kayan lambu sun ce kasuwa tana samun ƙarbuwa tare da bunƙasa, inda aka yi hasashen za ta iya kaiwa dala biliyan 1.15 a shekarar 2026.
Noman fure ya kasance muhimmin abin da ke samar da kudaden shiga daga kasashen waje, wanda ke tafiya kafada da kafada da ganyen shayi da kofi da kuma yawon bude ido, kana yana ba da gudummawar kusan kashi 18% na kudaden shigar da ake samu daga kayayyakin da ke fitarwa.
Furanni wardi ne suka fi mamaye fannin, inda suke samar da fiye da kashi 65 cikin 100 na yawan kudaden kayayyakin da ake fitarwa, kana ana dada samar da wasu irin furanni na lokacin rani kamar (Limonium, Solidago, Hypericum).
Yayin da ƙasashen kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta kasance babbar kasuwa mafi girma, Kenya ta fadada hanyoyi fitar ire-iren furanninta zuwa Gabas ta Tsakiya (Dubai) da China, wanda hakan ya rage dogaro da kasuwannin cikin gida.
A gefe guda kuma, Habasha ta ci gaba da kasancewa kasa ta hudu a duniya wajen fitar da furanni kuma kasa ta biyu a Afirka. Kasar za ta iya samar da furanni masu inganci a duk shekara, kuma akwai bukatar fadadawa samarwarta zuwa yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf.
Bangaren noman lambu ya kasance daya daga cikin manyan sassan samun kuɗaɗen waje ga Habasha, inda furanni ke ba da gudummawar kashi 80 cikin 100 na jimillar kudaden shigar da ake samu daga kayayyakin da ake fitarwa a fannin noma, sai kuma 'ya'yan itatuwa da sauran kayan lambu.
A kasafin kuɗin shekarar 2024 /25, ƙasar ta sami dala miliyan 564.9 daga tallafin hanyar amfani da fasahar noma ta zamani da hanyoyin da suka dace da yanayi, da kuma bin ƙa'idodin ƙasashen duniya, da kuma inganta damar shiga kasuwanni.
A wannan shekarar, bangaren fitar da furanni ya samar da dala miliyan 285.
A watan Satumba da Oktoban 2025, Bankin Ƙasa na Habasha da Ma'aikatar ayyukan Gona sun gabatar da mafi ƙarancin farashin furanni, gami da ƙarin kashi 7-11% ga gonakin furen wardi, da nufin haɓaka kuɗin shiga na ƙasashen waje.
An ƙayyade sabon tsarin farashi inda aka sa farashin furen (roses) a dala $4.57 kan kowace kilo ga gonakin tsaunuka, $4.76 ga yankunan tsaka-tsaki, da $5.12 ga yankunan ƙasa.
Masana’antar na faɗaɗa harkokinta fiye da furen wardi, inda yanzu ake mai da hankali kan “furannin rani” kamar ganyen eucalyptus a matsayin madadin da ya fi araha.
Kasashen Netherlands, Saudiyya, da Birtaniya su ne manyan wurare uku da Habasha ke fitar da furanninta zuwa.
Rikicin siyasa da tashin hankalin ƙabilanci, musamman a yankunan da ake noman furanni, sun daɗe suna shafar harkokin kasuwanci.
Yanzu haka, manyan ƙasashen da suka fi ƙarfin noman furanni a Afirka biyu na fuskantar raguwar kasuwanci mai tsanani sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.
Raguwar buƙata tare da tangardar jigilar kayayyaki zuwa Gabas ta Tsakiya da Turai ya sa, alal misali, ɓangaren noman furanni na Kenya ke asarar kusan dala miliyan 1.4 a kowane mako.
A ɓangaren Habasha kuma, masu ruwa da tsaki sun ce wasu gonaki da ke kai kayayyaki zuwa kasuwannin ƙasashen Larabawa sun fuskanci raguwar kudaden shiga har zuwa kashi 75 cikin 100.












