| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An kama mutum da kunamu 150 ɓoye a tufafinsa a filin jirgin sama na Afirka ta Kudu
Jami’ai sun gano wanda ake zargin ne ta hanyar amfani da kwatancen da aka bai waɗanda ke wurin kafin su kama shi su kuma bincika jakunkunansa.
An kama mutum da kunamu 150 ɓoye a tufafinsa a filin jirgin sama na Afirka ta Kudu
Za a gabatar da wanda ake zargin a gaban shari'a. / AFP

Hukumomi a Afirka ta Kudu sun kama wani mutum mai shekara 28 bayan an gano kunamu 150 rayayyu masu dafi, waɗanda aka ɓoye cikin tufafinsa a filin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa da ke Cape Town.

Hukumar ‘yansandan Afirka ta Kudu, (SAPS), ta ce an yi kamen ne ranar 12 ga Yuni a wani aiki da ɓangaren da ke yaƙi da safarar dabbobin masu fuskantar barazanar ƙarewa ya yi, bisa bayanan sirri da haɗin-gwiwar hukumar CapeNature mai kula da dabbobin daji.

Jami’ai sun gano wanda ake zargin ne ta hanyar amfani da kwatancen da aka ba su game da shi, kafin su kama shi su kuma bincika jakunkunansa.

Yayin binciken, hukumomi sun gano kunamu 150 masu dafi da ransu da ya ɓoye cikin tufafinsa. An kama wanda ake zargin bisa laifin riƙe namun daji ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya saɓa wa dokokin kare halittu da muhalli.

Hukumomi ba su gano inda matafiyin zai tafi ba tukuna ko kuma kimar kunamun da aka ƙwace a hannunsa, waɗanda har yanzu ana nazari kansu. An miƙa dabbobin ga ƙwararru domin tabbatar da tsaronsu da kuma ganin sun samu kulawar da ta dace.

Lamarin ya sake nuna yawan fasaƙwaurin namun daji a Afirka ta Kudu, wanda kasuwanci ne da bai tsaya kan sanannun halittun irin su karkanda da giwaye kawai ba, har wasu halittu da ba a sansu sosai ba ciki har dangogin ƙadangare da dangogin gizo, a kasuwar bayan fage ta ƙasa-da-ƙasa.

Ana sa ran wanda ake zargin zai bayyana a gaban kotun majistire ta Bellvill, domin fuskantar tuhume-tuhumen da za a yi masa.

Rumbun Labarai
Gwamnatin Mali ta tabbatar da kashe sojoji 30 a wani harin ta'addanci a arewacin ƙasar
Aikin matatar man Dangote zai ci gaba a gaɓar tekun  Kenya, a cewar Shugaba Ruto
Afirka ta sami tallafin $900m domin faɗaɗa fasahar girki na zamani mara gurɓata muhalli
Rasha na son ƙarfafa alaƙa da Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) - Lavrov
Sojojin Sudan sun ƙwace ƙauyen Al-Kurmuk bayan arangama da dakarun RSF
Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba fiye da 200
Ƙawancen tsaro na Turkiyya da Afirka na haɓaka a tsarin duniya da ke sauyawa
Jami’an leken asiri sun lalata yunƙurin ‘yan ta’addan Daesh na kai hari a garuruwan Morroco bakwai
'Yansandan Afirka Ta Kudu sun ce mutuwar ɗan Nijeriya ba ta da alaƙa da tashin hankalin ci-rani
MDD ta yi gargaɗin cewa hare-haren RSF na iya mayar da birnin Al-Obeid na Sudan kamar Al-Fasher
Rikicin diflomasiyya ya kaure tsakanin Ghana da Afirka ta Kudu kan mutuwar ɗan Ghana
Burkina Faso, Mali da Nijar sun gabatar da sanarwar ficewa daga ICC, in ji kotun
Sojojin Mali sun raka motocin dakon mai da abinci 940 zuwa Bamako saboda fargabar harin ta'addanci
Sojojin Burkina Faso sun ce sun kashe 'yanta'adda fiye da 400 a wani hari da suka daƙile
An gurfanar da ɗalibai mata takwas a kotu a Kenya kan zargin kisan abokan karatunsu a gobara
Yadda Nijeriya ke fama da hauhawar farashin gas din girki
MDD ta yi gargaɗin cewa cutar Ebola na iya jefa kusan mutane miliyan 1 cikin talauci a DRC
Afirka ta Kudu ta mai da fiye da mutum 25000 kasashensu kafin wa'adin 30 ga Yuni na masu ƙyamar baƙi
Yadda abinci ke yin kisan mummuƙe a Afirka
Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa