| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Asibitin Turkiyya ya kafa 'tarihin' zama na farko a duniya da aka yi dashen hanta da ta haɗa mutum 8
Turkiyya ta zama cibiyar dashen hanta ta duniya, wacce ta samu tallafi daga kwararrun likitoci na Jami'ar Inonu da ke yankin gabashin Anatolia, a cewar wani jami’in lafiya.
Asibitin Turkiyya ya kafa 'tarihin' zama na farko a duniya da aka yi dashen hanta da ta haɗa mutum 8
Ministan lafiyar Turkiyya ya jinjina wa Farfesa Sezai Yilmaz da tawagarsa daga Jami'ar Inonu saboda gudanar da aikin dashen hanta. / TRT Afrika Hausa

Wata tawagar likitocin Turkiyya ta yi dashen hanta na farko a duniya wa mutane takwas a lokaci daya, kamar yadda minsitan lafiya na ƙasar ya bayyana a ranar Talata.

Ministan lafiyar kasar Kemal Memisoglu ya yaba wa Farfesa Sezai Yilmaz da tawagarsa daga Jami'ar Inonu bisa ƙokarin da suka yi wajen aiwatar da aikin, inda ya kira shi wani muhimmin ci gaba a tarihin harkokin lafiya a ƙasar.

"An kafa wani sabon tarihi a duniya a karon farko a Cibiyar dashen hanta ta Jami'ar Inonu," in ji Memisoglu.

Dr. Sezai Yilmaz da tawagarsa sun sanya sunayensu a kambun tarihin lafiya inda suka yi dashen hanta kan majinyata 8.’’

Ya ce Turkiyya ta zama cibiyar sani da ta yi fice a duniya wajen dashen hanta, jinjina ga masana kimiyya da kuma kwararrun likitoci da aka horar a Jami'ar Inonu, wacce ke yankin gabashin Anatolia.

A cewar Memisoglu, ana gudanar da dashen hanta kusan 1,800 a kowace shekara a Turkiyy, inda ake gudanar da fiye da 300 a cibiyar.

Kazalika ya yaba wa tawagar likitocin tare da jinjina musu bisa gudunmawar da suka bayar ga ci gaban kiwon lafiya da kimiyyar likitanci a duniya.