| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Nijeriya, Senegal da Libya sun buƙaci a tsagaita wuta yayin da Isra'ila-Amurka ke rikici da Iran
Hare-haren haɗin gwiwar da Amurka da Isra'ila suka kai a kan Iran sun jefa duniya cikin fargaba.
Nijeriya, Senegal da Libya sun buƙaci a tsagaita wuta yayin da Isra'ila-Amurka ke rikici da Iran
Hoton bayan harin Isra'ila kan wata makaranta a Minab, inda hukumomin Iran suka ce an kashe yara fiye da 100. / Reuters
1 Maris 2026

Gwamnatoci da kungiyoyi na ƙasa da ƙasa a fadin duniya sun nuna matuƙar damuwa yayin da tashin hankali a Gabas ta Tsakiya ya ƙaru bayan harin sojin Amurka da Isra'ila a kan Iran.

An yi kira da a tsagaita wuta tare da bin dokokin ƙasa da ƙasa, inda ake nuna tsoro kan yiwuwar bazuwar rashin zaman lafiya a yankin da kuma damuwar haddasa rikice-rikice ga tattalin arzikin duniya.

Ƙasashe ciki har da Aljeriya, Libya, Nijeriya, Senegal da Kazakhstan sun yi Allah wadai da ƙarin tashin hankalin da ake samu kuma sun buƙaci a nemi mafita ta hanyar diflomasiyya.

Aljeriya ta ce ta “yi matukar baƙin ciki” saboda ƙaruwar fargabar ayyukan soja a wasu sassan ƙsashen Larabawa kuma ta yi kira ga duka ɓangarorin da su ɗauki alhakin abubuwan da ke faruwa tare da daƙile faɗaɗarsa.

Libya ta kira hare-haren Isra'ila “abubuwan da ba za a amince da su ba”, inda ta jaddada cewa ya kamata a magance rikice-rikice ta hanyar tattaunawa mai amfani maimakon matakan soja, tare da bayyana cewa keta 'yancin ƙasa a ƙasashe kamar Saudiyya, Qatar, Syria, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Kuwait, da Jordan ya saɓawa ƙa'idojin kyakkyawar zamantakewa ta makwabta.

Ghana ta fara kwashe ma'aikatan ofishin jakadancinta

Tuni wasu kasashe kuma suka fara ɗaukar matakan kariya don kare 'yan kasarsu.

Ghana ta fara wani ɓangaren fitar da ma'aikatan ofishin jakadancinta a Tehran kuma ta shawarci 'yan kasar da ke Bahrain, Isra'ila, Kuwait, Qatar da UAE su kasance a cikin gida, su guji wuraren taro da yawa kuma su ci gaba da kasancewa cikin tuntuba da ofisoshin diflomasiyya.

Nijeriya ta yi gargaɗi cewa ƙaruwar hare-hare na iya haifar da mummunar illa ga yankin da ma duniya baki ɗaya, inda ta yi kira ga ƙasashe su fifita tattaunawa, su guji matakan da za su ƙara tashin hankali sannan su girmama dokokin ƙasa da ƙasa.

Senegal ta yi Allah wadai da amfani da ƙarfi kuma ta kira da a yi gaggawar tsagaita wuta, tana mai cewa diflomasiyya ita ce hanya kaɗai mai tushe zuwa sulhu mai ɗorewa.

Kwamitin Hukumar Tarayyar Afirka (African Union Commission) shi ma ya yi Allah wadai da harin makamai da jiragen kamikaze na Iran a matsayin keta 'yancin ƙasa wanda zai iya kara dagula yanayin Gabas ta Tsakiya.

Kwamitin ya yi kira da a yi gaggawar kwantar da wannan rikici da komawa ga diflomasiyya, yana tabbatar da jajircewarsa ga zaman lafiya, bin dokokin ƙasa da ƙasa da warware saɓani ta hanyar tattaunawa.

Ƙungiyar ECOWAS ta daidaita bayaninta da na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, inda ta jaddada cewa ƙaruwar ayyukan soja na iya dagula Gabas ta Tsakiya, tayar da hankali a kasuwannin makamashi na duniya, hana cinikayya da toshe hanyoyin samar da abinci, da raunana zaman lafiya da tsaro a duniya.

An rufe sararin samaniya

Tashin hankalin ya fara da sassafe a ranar Asabar lokacin da Isra'ila da Amurka suka kai farmakin haɗin gwiwa a kan birane da dama a Iran, ciki har da Tehran, Isfahan, Karaj, Qom, Tabriz, Bushehr, Kermanshah da Ilam.

Isra'ila ta bayyana aikin a matsayin “harin rigakafi”, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da “manyan ayyukan yaki” a kan Iran.

Isra'ila da Iran sun rufe sararin samaniyarsu. Isra'ila ta ayyana dokar ta-ɓaci an kuma yi kira ga fararen-hula su nemi mafaka yayin da ake jiran martanin Iran.

Iran ta bayar da rahoton harba ɗaruruwan makamai masu linzami zuwa Isra'ila kuma ta kai hari kan manyan sansanonin Amurka a Bahrain, UAE, Kuwait, Qatar da Jordan ta amfani da makamai da jiragen kamikaze.