Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Nijeriya na cewa an kashe aƙalla sojoji 11 da wani ɗansanda a wani harin kwanton-ɓauna da ‘yanta’adda na Lakurawa suka kai musu a garin Giro Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga.
Harin ya auku ne ranar Talata da daddare yayin da jami’an tsaro suka bi sawun ‘yanta’adda zuwa harabar ofishin wani kamfanin gine-gine bayan sun samu bayanan sirri cewa ‘yanbindiga suna taruwa a wurin.
Sai dai kuma a kan hanyarsu ta zuwa wurin, ‘yanta’addan sun yi musu kwanton-ɓauna.
“Na ji labarin kwanton-ɓaunar da ‘yanta’adda suka yi wa sojinmu. Rundunar sojin ta samu bayanai na neman ɗauki ne cewa ‘yanbindiga na shirin kai hari kan ɗaya daga cikin garuruwanmu. Kuma sojoji suka shirya domin zuwa su tsare mutanenmu,” kamar yadda gwamnan jihar, Nasir Idris, ya bayyana yayin da ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru tare da Sarkin Yauri, Alhaji Zayyanu Abdullahi.
“Amma, bayanan da aka bai wa sojinmu cewa suna taruwa a wani wuri ba gaskiya ba ne,” in ji gwamnan.
A kwanton-ɓaunar da ‘yanta’addan suka yi sojojin a kan hanyarsu, aƙalla sojoji 11 da ɗansandan ɗaya suka rasa rayukansu, kamar yadda jaridar Daily Trust da sauran jaridun Nijeriya suka ruwaito.
Rahotannin sun ƙara da cewa maharan sun ƙona motocin soji biyu.
Gwamnan Jihar Kebbi ya ziyarci ɓangaren ba da kulawar gaggawa na Asibitin Koyarwar gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi inda aka kwantar da mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Da yake magana da ‘yanjarida bayan ziyarar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin taƙaici da dabbanci.
Ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin jihar za ta biya kuɗin jinyar waɗanda suka jikkata a lamarin tare da ba da tallafi ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu.
Ya ce, “Kowa ya san cewa gwamnatin jihar Kebbi ba ta wasa da lamuran tsaro. Mun zo nan ne don mu ga abubuwa da kanmu. Kuma mun ba da umarni ga babban daraktan asibitin ya tabbatar da cewa sun yi abin da ya kamata ga waɗanda suka jikkata.
“Kazalika, ga waɗanda suka rasa rayukansu, gwamnatin jihar Kebbi za ta yi duk abin da ya dace domin tallafa wa iyalansu. Wannan babban rashi ne kuma abin alhini ne sosai. Amma mun rungumi ƙaddara.
“Waɗannan sojoji ne da ke kare rayukan mazauna Kebbi, duk da haka sun samu kansu a cikin irin wannan hali. Gwamnatin jihar Kebbiba ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarinta na kare rayukan ‘yan jihar.
“Mun tausaya wa sojiji 11 da ɗansanda ɗaya da suka rasa rayukansu a wannan lamari”, in ji shi.
Gwamnan ya bayyana ‘yan ƙungiyar Lakurawa a matsayin marasa tausayi kuma ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa ƙoƙarin tsaro. Ya kuma ɗauki alƙawarin ganawa da babban hafsan tsaron Nijeriya a Abuja game da lamarin.
“Za mu maye gurbin motocin aiki biyu da ɓarayin dajin suka ƙona,” in ji shi
Idris ya yaba wa jami’an sojin kan ƙoƙarinsu kuma ya yi kira gare su su ci gaba da dagewa.
“Na gode wa rundunar sojin da yin iya ƙoƙarinta da kuma mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Kada ku bari wannan lamarin ya sa ku ja da baya; ku ci gaba da nuna ƙwarewa a aiki,” kamar yadda ya shaida wa sojojin.
Hare-hare masu muni
‘Yanbindiga da ‘yanta’adda suna kai hare-hare a arewacin Nijeriya inda a wasu lokutan lamarin ke janyo rasa rayukan wasu daga cikin dakarun Nijeriya.
Ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 2025, rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji 17 a wani bata-kashin da suka yi da ‘yanfashin daji a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Dakarun sun nemi kai ɗauki ne bayan sun sami rahoton kai hari kan garin Bangi inda suka yi arangama da wasa mayaƙa masu makamai da yawa, lamarin da ya janyo rasa rayukansu, kamar yadda kafar Channels ta ruwaito.
A arewa maso gabashin ƙasar kuwa, hare-haren ‘yanta’adda na ci gaba babu ƙaƙƙautawa inda ‘yanta’adda na Boko Haram da ISWAP ke kai hare-haren kan sansanonin soji, lamarin da ke sa wasu sojoji su rasa rayukansu.
Irin wannan batun ya faru a ƙarshen shekarar 2025, a lokacin da wasu dakaru suka rasa rayukansu yayin wani samame da ‘yanta’adda suka kai kan wani sansanin soji.











