Nijeriya za ta buga wasan sada zumunta da Iran a Maris ɗin nan

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles za ta buga wasan sada-zumunta da takwararta ta Iran, kamar yadda aka shirya. Sai dai batun yaƙin da ake tsakanin Iran da Amurka-Isra'ila zai iya kawo tarnaƙi.

By
Wasan ƙarshe da Nijeriya da Irana suka buga tsakaninsu shi ne na zagayen rukuni a gasar Kofin Duniya na 2014, inda aka tashi 0-0. / CAF

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta sanar da jerin wasannin sada zumunta da babbar tawagar ƙasar, Super Eagles za ta buga tare da ƙasashe uku da za a fara a watan Maris ɗin nan.

Super Eagles za ta buga wasannin sada zumuntar na gayyata a birnin Amman da ke Jordan. Kuma an shirya buga wasannin lokacin hutun FIFA na wasannin ƙasa-da-ƙasa na Maris ɗin nan.

Ranar 27 ga Maris Super Eagles za ta buga wasan da takwararta ta Iran, kamar yadda jadawalin wasannin ya nuna. Sai ranar 31 ga Maris, Nijeriya ta kara da Jordan. Sauran ƙasashen biyu su ne Jordan mai masaukin baƙi, da kuma Costa Rica.

Ga Nijeriya, wasannin za su zama na share fagen wasannin neman cancantar buga gasar Kofin ƙasashen Afirka na 2027, inda koci da jami’an wasa za su samu damar tantancewa da zaɓar ‘yanwasa.

Wasannin na zuwa ne yayin da ya rage watanni uku a a fara gasar kofin duniya na FIFA 2026 a ƙasashen Amurka, Mexico, da Canada. Amma a yanzu Nijeriya ba ta cancanci shiga gasar ba.

Batun yaƙi da na Kofin Duniya

Sai dai kuma, a ƙarshen makon jiya ne aka fara gwabza yaƙi tsakanin Iran da Amurka-Isra’ila, inda ake kai hare-hare a Iran har aka kashe jagoran addini na ƙasar, kuma ake zaman makokin kwana 40.

Baya ga batun yaƙin, masu sharhi na yin tambaya kan dacewar shigar Nijeriya wasannin sada zumunta bayan kuma akwai batun yiwuwar shigarta gasar Kofin Duniya.

Hukumar Ƙwallon Nijeriya, NFF tana da ƙorafi a wajen hukumar FIFA kan zargin Congo DR ta yi amfani da ‘yanwasan da ba su cancanta ba a wasan cike gurbin cancantar buga gasar, wadda Congo ta doke Nijeriya.

Wasannin na sada zumunta za a buga su daidai lokacin da ake buga wasannin cike gurbi na shiga kofin duniya. Kuma idan aka ce Nijeriya ta yi nasara a ƙararta, kenan dole ta shiga wasannin cike gurbin na kofin duniya.

Irin wannan ta faru a Nuwamban bara, lokacin NFF ta shirya wasanni biyu na sada zumunta da Super Eagles za ta yi a Amurka, gabanin samun cancantar buga wasannin cike gurbi na CAF. Da ta samu shiga wasannin cike gurbin, sai aka soke wasannin sada zumuntar.

Sai dai kuma, a wannan karon wasannin sada zumuntar za a yi su cikin rukuni mai ƙunshe da ƙasashe huɗu. Don haka soke wani wasa zai yi zama mai wahala.