| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Wakiliyar MDD kan 'yancin addini ta fara ziyarar aiki a Nijeriya
Nazila Ghanea, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan ’yancin addini ta isa Nijeriya a ranar Litinin domin gudanar da wata ziyara da za ta kai zuwa Abuja, Kano, da kuma Jos a Jihar Filato.
Wakiliyar MDD kan 'yancin addini ta fara ziyarar aiki a Nijeriya
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan ’yancin addini Nazila Ghanea / Others

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan ‘yancin addini ta fara wata ziyarar aiki ta makonni biyu a Nigeria a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce a duniya dangane da ‘yancin addini da kuma matsalolin tsaro a ƙasar ta Afirka mafi yawan jama’a.

Nazila Ghanea, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan ’yancin addini ta isa Nijeriya a ranar Litinin domin gudanar da wata ziyara da za ta kai zuwa Abuja, Kano, da kuma Jos a Jihar Filato.

Ziyarar tata na zuwa ne bayan shekara guda da aka shafe ana fuskantar takun-saka na diflomasiyya sakamakon zarge-zargen cewa Kiristoci a Nijeriya na fuskantar tsangwama.

Batun ya ja hankalin duniya bayan wasu ƙungiyoyin siyasa da na addini a Amurka sun zargi gwamnatin Nijeriya da gaza kare al’ummomin Kirista.

Daga baya wasu manyan jami’an Amurka sun maimaita waɗannan zarge-zarge, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi a cikin Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Wannan ce-ce-ku-ce ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro da Nijeriya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci masu alaƙa da Daesh-WAP da sauran ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da ke aiki a yankin Afirka ta Yamma.

Sai dai masana da masu sa ido masu zaman kansu da dama sun ce yanayin tsaro da addini a Nijeriya ya ya sha bamban da yadda ake yawan bayyana shi.

Ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da Deash-WAP sun shafe shekaru suna kai hare-hare masu muni, musamman a arewacin Nijeriya.

Duk da haka, masana sun lura cewa da yawa daga cikin waɗanda hare-haren ke kashewa Musulmi ne, kasancewar mafi yawan tashin hankalin na faruwa ne a yankunan da Musulmi suka fi rinjaye.

Hare-haren baya-bayan nan sun nuna hakan. Hare-haren kunar bakin wake a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun afka wa wata kasuwa mai cunkoso da kuma wani masallaci daga baya, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayukan fararen hula da dama.

Hukumomi sun ɗora alhakin hare-haren kan Boko Haram.

Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta bayyana cikakken abin da ziyarar Ghanea za ta ƙunsa ba, sai dai ta ce za ta tantance ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu da kuma waɗanda ke tasowa dangane da ’yancin addini da akida a Nijeriya.

Nijeriya, wadda ke da kusan mutane miliyan 230, ta kasu kusan daidai tsakanin yankin kudu mai rinjayen Kiristoci da yankin arewa mai rinjayen Musulmi.

Duk da wasu lokuta na tashin hankali, miliyoyin ’yan Nijeriya masu mabambantan addinai suna rayuwa da aiki tare cikin zaman lafiya.

Sai dai ƙasar ta sha fama da rikice-rikicen addini da na al’umma a wasu lokuta. Manyan rikice-rikice a wurare kamar Jos a shekarar 2008 da Mangu a shekarar 2024 sun nuna yadda sabanin da ya shafi addini, ƙabila, mallakar ƙasa da wakilcin siyasa kan iya rikidewa zuwa tashin hankali mai jawo asarar rayuka.