'Yansanda a Nijeriya sun kama mutum 33 kan zargin satar mutane a coci

Hukumar 'yansanda a Nijeriya sun ce sun kama wani gungun mutum 33 da ake zargi da hannu a satar mutane 38 daga coci, lamarin da ya faru a Nuwamban 2025.

By
'Yan sanda Najeriya sun kama mutane 38 da ake zargi kan sace-sacen mutane da aka yi a wata coci a jihar Kwara a watan Nuwamba 2025. / AP

'Yansandan Nijeriya sun ce sun kama wani gungun mutum 33 da ake zargi da hannu a sace mutane 38 daga wani coci a watan Nuwamban 2025.

Harin da aka kai kan Cocin Christ Apostolic a garin Euruku na jihar Kwara ta tsakiyar Najeriya, ya ɗauki hankali lokacin da aka nuna lokacin da ake ibada kai-tsaye ta intanet, inda bidiyo ya nuna masu ibada suna gudu saboda harbin bindiga.

Dukkanin mabiyan cocin su 38 da aka sace, an ceto su 'yan kwanaki daga bisani.

Mai magana da yawun 'yansandan Nijeriya, Anthony Okon Placid, ya faɗa ranar Talata cewa, "'yan ƙungiyar da aka kama suna da alhakin aikata ta'addanci, (da) satar shanu."

Barazanar ta'addanci

Yawancin yankunan karkara na Kwara suna fuskantar ƙaruwar hare-hare na tashin hankali a 'yan watannin da suka gabata, inda mafi ƙungiyoyin 'yanta'adda ne ke aikata su.

'Yanbindiga sun sace aƙalla mazauna karkara su 10 a Isapa, wani gari da ke makwabtaka, kusan sati guda bayan lamarin Euruku.

Haka ma a watan Fabrairu da ya gabata, 'yanta'adda sun kashe aƙalla mutane 162 a ƙauyen Woro.