Jagoran ƴan-awaren Biafra: Babbar Kotu a Nijeriya ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai

Alƙalin kotun ya ce masu shigar da ƙara sun kawo shaidun da suka nuna cewa Nnamdu Kanu ya tunzura munanan hare-haren kan jami'an tsaro da kuma 'yan Nijeriya da ke kudu maso gabashin Nijeriya.

By
An kama Kanu a karon farko a 2015, amma ya tsere daga Nijeriya yayin da yake a kan beli a 2017.

Wata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya a ranar Alhamis ta yanke wa jagoran ‘yan-awaren Biafra Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai.

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan shafe shekaru ana gudanar da shari’ar Mista Kanu.

Mai Shari’a James Omotosho wanda ya yanke hukuncin ya bayar da umarni kan a saka ido kan Kanu a gidan yari sannan kada a ba shi damar amfani da waya ko kuma wata na’urar sadarwa.

Alkalin ya ce ko da za a bayar da wannan damar ga Kanu sai da sahalewa da kuma sa ido na ofishin babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Tun da fari gabanin yanke hukuncin, Alkalin ya ce ya samu shugaban 'yan-aware da ke fafutukar kafa ƙasar da laifukan da suka shafi ta'addanci.

Omotosho ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da cewa maganganun da Kanu ya yi a rediyo da umarnin da ya bayar daga ƙungiyarsa ta Indigenous People of Biafra (IPOB) wadda a yanzu aka haramta ayyukanta, sun haddasa hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro da fararen-hula a yankin kudu maso gabas a cikin ƙoƙarinsa na neman kafa ƙasar Biafra mai cin gashin kanta.

Yunkurin yankin na ɓallewa a matsayin Jamhuriyar Biafra a 1967 ya haifar da yaƙin basasa na shekaru uku wanda ya kashe fiye da miliyan ɗaya.

An kama Kanu a karon farko a 2015, amma ya tsere daga Nijeriya yayin da yake a kan beli a 2017.

Daga bisani an sake kama shi a Kenya a 2021, sannan aka tuhume shi a Nijeriya da laifukan ta'addanci guda bakwai. Kanu ya musanta waɗannan tuhume-tuhumen.