| Hausa
SIYASA
3 minti karatu
Nijar ta ce sojoji 'yantawaye ne suka ƙaddamar da hare-hare a babban birnin ƙasar Yamai
Rikici ya ɓarke a Yamai babban birnin Nijar ranar Asabar tsakanin dakarun da ke tsaron shugaban ƙasa da wasu sojoji bayan an shafe dare ana harbe-harbe a sassan birnin.
Nijar ta ce sojoji 'yantawaye ne suka ƙaddamar da hare-hare a babban birnin ƙasar Yamai
Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Mody / Facebook/CNSP

Ma’aikatar tsaron Nijar ta bayyana ranar Asabar cewa sojoji ‘yantawaye daga wani sansanin soji a Yamai ne suka buɗe wuta kan "muhimman wurare" a birnin, lamarin da ya tabbatar da cewa hare-haren da aka shafe sa’o’i ana kaiwa sojoji ne suka kai su.

Kamfanonin dillancin labarai ciki har da AFP da AP da Reuters sun ruwaito cewa wata sanarwa da ministan tsaron ƙasar, Janar Salifou Mody ya sanya wa hannu kuma aka karanta a gidan talabijin na ƙasar ta ɗaura alhaƙin hare-haren da aka kai birnin ne kan sojoji ‘yantawaye.

Rikici ya ɓarke a Yamai babban birnin Nijar ranar Asabar tsakanin dakarun da ke tsaron shugaban ƙasa da wasu sojoji, bayan an shafe dare ana harbe-harbe a sassan birnin.

"Wasu masu tayar da ƙayar baya daga cikin dakarun sojin Nijar sun yi ƙoƙarin shiga fadar shugaban ƙasa," kamar yadda wata majiya ta tsaro ta shaida wa AFP.

"Rundunar tsaron shugaban ƙasa ta tura su baya. Ana ci gaba da musayar wuta a fadar ."

Wani jami’in diflomasiyyar Afirka a Yamai ya ce zuwa yanzu rundunar tsaron shugaban ƙasar na biyayya ga shugaban ƙasar Janar Abdourahamane Tiani.

Rundunar sojin ƙasar ta ce "sannu a hankali" tana sake karɓar iko bayan sojoji ‘yantawaye sun yi garkuwa da sojoji a wani sansani kusa da filin jirgin saman babban birnin ƙasar.

A wata sanarwar da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar kuma ministan tsaron ƙasar Janar Salifou Mody ya sanya wa hannu, hukumomin sun yi kira ga mutanen ƙasar su "kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da harkokinsu a tsanake".

An fara buɗe wuta ne da sanyin safiyar ranar Asabar, lamarin da ya sa rundunar sojin ƙasar ta fitar da sanarwa a kan shafukan sada zumuntanta inda take kira ga mutane su kwantar da hankulansu kuma "su ƙaurace wa yaɗa labarai da ba a tantance ba ".

"An tattara dakarun tsaronmu domin kare ƙasarmu," in ji sanarwar.

Wani mazaunin birnin ya shaida wa AFP cewa an samu "harbe-harbe da fashe-fashen abubuwa masu ƙara sosai" a sansani na 101 a Yamai, wani rahoton da wasu shaidu suka tabbatar.

Gidan talabijin na ƙasar Tele Sahel ya ɗauke na lokacin da ya zarce sa’a ɗaya, a kan intanet da tauraron ɗan adam. Sai da misalin ƙarfe 10:00 na safe (ƙarfe 0900 agogon GMT) gidan talabijin ɗin ya dawo aiki.

Sojoji sun toshe hanyar shiga fadar shugaban ƙasar da gidan talabijin na ƙasar, kamar yadda mazauna ƙasar suka bayyana.

An fara jin ƙarar harbe-harbe ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare kuma harbe-harben sun ci gaba har zuwa safiya, in ji wani ɗan jaridan ƙasar da ke ɗaukar bidyo a wani wurin da ke kusa da filin jiragen saman.

Wani mazaunin garin kuma ya ce ya ji "harbe-harbe" da misalin ƙarfe 7:00 na safiya.

"Na je saka kuɗi a wayata. Na ga wata motar soji wadda ke tafiya sansanin ta juyo," in ji shi.

"Makaman da muke ji ba irin waɗanda ‘yanta’addan da ke bisa babura suke amfani da su ba ne. Ana yaƙi babu ƙaƙƙautawa tun daren jiya."

Wani mazaunin yammacin Yamai kuma ya ce shi ya ji harbe-harbe da misalin ƙarfe 5:00 na safiya.

Saƙonnin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun ba da rahoton harbe-harbe da fashe-fashen abubuwa a birnin, musamman a unguwar da gine-ginen gwamnati suke inda fadar shugaban ƙasa da kuma gidan talabijin na ƙasa suke.

Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motoci masu sulke da aka tura domin kai ɗauki a unguwar da ke kusa da filin jiragen saman.