Eid al-Fitr: Hotunan yadda aka yi bikin ƙaramar Sallah a ƙasashen Afirka

An soma ranar ce da gudanar da sallar Idi sannan aka shiga shagulgula da suka haɗa da ziyarce-ziyarce da saka sabbin tufafi da sauran ayyukan alheri.

By
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya jagoranci sauran al'umma wajen yin Idin karamar sallah / Kano State Government

Musulmai a faɗin ƙasashen Afirka sun bi sahun sauran Musulman duniya wajen gudanar da bukukuwan Eid al-Fitr, wato ƙaramar sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.

An soma ranar ce da gudanar da sallar Idi sannan aka shiga shagulgula da suka haɗa da ziyarce-ziyarce da saka sabbin tufafi da sauran ayyukan alheri.

Shugabannin ƙasashe da na al’umma sun yi kira ga jama’a su aiwatar da abubuwan da suka koya a watan Ramadan.

Ga hotunan yadda aka yi bukukuwan sallah a wasu ƙasashen Afirka: