Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta tarwatsa wata babbar ƙungiya ta masu haƙa da samar da miyagun ƙwayoyi ta methamphetamine da aka bayyana a matsayin mafi girma da aka taɓa ganowa a Najeriya.
Hukumar ta kama wani shahararren shugaban ƙungiyar, ’yan Mexico uku da kuma ’yan Nijeriya shida yayin wani gagarumin samame da aka gudanar a jihohin Ogun da Lagos.
Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda ya ce wannan aiki ya yi wa manyan ƙungiyoyin aikata laifukan ƙetare iyaka mummunar illa.
Ya ce an gudanar da aikin ne bayan shafe watanni ana tattara bayanan sirri, inda jami’an sashen musamman na hukumar suka kai samame a wani dakin samar da methamphetamine da ke ɓoye a cikin dajin Abidagba, cikin ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas a jihar Ogun, inda aka kama masu laifin suna sarrafa miyagun ƙwayoyi a matakin masana’antu.
Daga cikin waɗanda aka kama a dajin akwai ’yan Nijeriya huɗu da kuma ’yan Mexico uku da ake zargin an shigo da su Nijeriya domin su taimaka wajen fasahar samar da wannan muguwar ƙwaya.
Marwa ya ƙara da cewa wani rukuni na jami’an tsaro sun kuma kai farmaki gidan shugaban ƙungiyar da ke Lekki a jihar Lagos, inda aka bayyana shi da sunan Anochili Innocent, wanda ake zargi da kasancewa jagoran ƙungiyar.
A yayin farmakin, an ce jami’an sun gano fasfo da wayoyin hannu na ’yan Mexico da aka kama, abin da ya ƙara tabbatar da alaƙarsa da shigo da su da kuma tafiyar da aikin ƙungiyar.
Hukumar ta bayyana cewa bayan wannan farmaki, an kuma kama wasu mutum biyu tare da gano wani gidan da ake amfani da shi wajen ɓoye kayan miyagun ƙwayoyi.
Jimillar abin da aka kama ya kai kilo 2,419 na methamphetamine da sinadarai masu haɗari, wanda darajarsa ta kai kusan dala miliyan 362.9, wato sama da Naira biliyan 480.
A ƙarshe, Marwa ya yi gargaɗi cewa Nijeriya za ta ci gaba da zama ƙasa mai tsauri ga masu safarar miyagun ƙwayoyi, inda ya jaddada cewa hukumar ba za ta daina bin sawunsu ba har sai ta tarwatsa dukkanin ƙungiyoyin da ke wannan aiki.
Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su riƙa ba da rahoton duk wani abin da suke zargi domin taimakawa yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi.













