| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Adadin ɗaliban da suka mutu a hatsarin motar Uganda ya kai 23
Bas ɗin na kan hanyarta ta dawowa babban birnin ƙasar, Kampala, daga wata tafiya ta makaranta zuwa wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls a gabashin Uganda ranar Alhamisa lokacin da motar da kauce daga kan hanya.
Adadin ɗaliban da suka mutu a hatsarin motar Uganda ya kai 23
Dalibai sun mutu a hatsarin motar Uganda

Adadin waɗanda suka mutu daga hatsarin bas ɗin ‘yanmakaranta a Uganda ya ƙaru zuwa yara 23 da wani babban mutum ɗaya, kuma an dakatar da dukkan tafiye-tafiye na makaranta, kamar yadda ‘yansanda suka bayyana a ranar Jumma’a.

Ƙasar ta gabashin Afirka tana yawan samun haɗɗura na bas da manyan motoci a kan manyan hanyoyi.

Bas ɗin tana kan hanyarta ta dawowa babban birnin ƙasar, Kampala, daga wata tafiya ta makarantar zuwa wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls a gabashin Uganda ranar Alhamis ne a lokacin da motar ta kauce daga kan hanya, inda ta kashe ɗalibai 20 da wani balagagge.

Tun wancan lokacin “ƙarin ɗalibai uku sun mutu sakamakon raunukan da suka ji a hatsarin yayin da suke karɓar magani a asibiti", in ji ‘yansanda.

Kawo yanzu ba gane shida daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu ba.

Direba ya kauce wa hanya

Direban, wanda ake tunaniin ya ji munanan raunuka, rahotannui sun ce ya kauce a kan hanya ne, kuma ya daki wani babban dutse kana motar ta kife, in ji ‘yansanda.

Ranar Jumma’a, ma’aikatar ilimin ƙasar ta kira wani zama na gaggawa kuma ta yi shelar dakatar da dukkan tafiye-tafiye na makaranti a faɗin ƙasar .

Katse tafiye-tafiyen ya zo ne domin ba da damar "cikakken bincike cikin yanayin da ya haddasa haɗɗuran kwanannan nan da ke da alaƙa da ‘yan makaranta,” da inganta matakan tsaro da kuma ba da horaswa na tsaro ga makaranti da kamfanonin sufuri, in ji ‘yansanda.

Ana kan bincike

Bala’in ya auku ne kusa da Kaserem, fiye da kilomita 250 (mil 150 ) daga Kamapala, tsakanin Kapchorwa, inda wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls ya ke, da kuma birnin Mbale.

‘Yansanda sun fitar da wani hoto da wata bas da ta magale kum ata kife tare da bayyana cewa an fara gudanar da bincike.

Ashirin da uku daga cikin wdnada suka ji rauni suna asibiti kawo yanzu.

Saura motoci uku da suke cikin tafiyar ‘yan makarantar King David Junior School a Kampala sun koma lafiya, in ji ‘yansanda.

Akan samu haɗuran motoci a Uganda. A watan Oktoba, motocin bas biyu sun yi karo a kan wata babbar hanya, inda suka kashe aƙalla mutum 46.

Wani rahoto na shekarar 2024 ya ce an samu taho-mu-gaman motoci 4,434 da mace-mace 5,144 a cikin shekarar.

Rumbun Labarai
Yankuna uku na Ghana za su fuskanci katsewar wutar lantarki, in ji kamfanin ECG
Abubuwa biyar da kuke buƙatar sani game da zaɓen Zambia na ranar 13 ga Agusta
Fiye da mutum 5000 sun tsere saboda rashin tsaro da ke daɗa ƙamari a Darfur ta Yamma a Sudan: MDD
Daga Chibok zuwa yau: Me ya sa har yanzu makarantun Nijeriya ba su da tsaro?
Hatsarin mota ya kashe mutum 22, ciki har da sojoji 17 a Nijar
An roƙi Chadi ta janye matakinta na ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka
Uganda za ta tura sojoji domin aiki a yankin Gaza
Kenya na binciken abin da ake tunanin guba ce wadda ta kashe giwaye 16
Guinea ta nemi Faransa ta mayar da ƙoƙon kawunan 'yan ƙasarta masu fafutuka
Ƙoƙarin kawar da sankarau: Manufar Afirka ta kawar da cutar baki ɗaya nan da 2030
Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati
Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abinci a makare da illolin shan siga da giya
Shugaba Biya na Kamaru ya yi sauye-sauye a shugabancin sojin ƙasar
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Ɗaruruwan mutane sun yi hijira daga kudu maso yammacin Nijar saboda hare-haren 'yanta'adda
‘Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar, in ji kafar watsa labaran gwamnati
Fitacciyar mawaƙiyar Afirka Ta Kudu ta soke kalankuwarta a Legas bayan an kori baƙi daga ƙasarta
Gwamnatin Ghana ta amince da shawara ƙara wa'adin mulkin shugaban ƙasa
Adadin 'yan ci-ranin da suka rasu ya kai 19 bayan dubbai sun tsallaka zuwa yankin Ceuta na Sifaniya