| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Messi ya ce Argentina za ta "maimaita nasarar" cin Kofin Duniya
Da aka tambaye shi game da yadda yake ji bayan buga wasan sada-zumunta gabanin fara Kofin Duniya, Messi ya nuna farin cikinsa da yadda ya samu sauƙi bayan jinyar da ya yi.
Messi ya ce Argentina za ta "maimaita nasarar" cin Kofin Duniya
Argentina ce ta lashe Kofin Duniya na 2022. / Reuters

Yayin da za a buɗe gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 a wannan makon, gwarzon ɗanwasan Argentina, Lionel Messi, ya bayyana kyakkyawan fatansa na sake kai ƙasarsa ga nasarar lashe Kofin Duniya.

A gasar ta ƙarshe da ta gudana a Qatar, Argentina ce ta lashe kofin, kuma a gasar bana da za a buɗe ranar Alhamis 11 ga Yuni a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico, ƙasar na burin maimaita hakan.

Yau Laraba ne Argentina ta buga wasan sada-zumunta da Iceland, inda ta lashe wasan da ci 3-0, inda Messi ya ce ƙwallo ɗaya a minti na 70 kuma ya kafa sabon tarihin cin ƙwallaye mafi yawa, har 117 ga ƙasarsa.

Messi yana da shekaru 38, da wata 11, da kwana 14, wanda ke nufin ya zama ɗanƙwallo mafi tsufa da ciyo wa Argentina ƙwallo, inda ya wuce tsohon ɗanwasan ƙasar, Angel Labruna da ya kafa tarihin tun a 1957.

Maimaita nasara

A wannan wasan da Messi ya buga wa ƙasarsa a karo na 199, Messi ya zama ɗanwasan da ya fi yawan taka wa Argentina leda a tarihi.

Sai dai har yanzu Labruna ne mafi tsufan ɗanwasan da ya buga wa Argentina Kofin Duniya, lokacin yana da shekara 39 da kwana 260 a 1958, kuma Messi ba zai iya rushe wannan tarihin ba a bana.

Da aka tambaye shi game da yadda yake ji bayan buga wasan sada-zumunta gabanin fara Kofin Duniya, Messi ya nuna farin cikinsa da yadda ya samu sauƙi bayan jinyar da ya yi.

Game da Kofin Duniya, Messi ya bayyana cewa, “Kamar yadda aka saba, duk sanda gasa ta fara, musamman ta Kofin Duniya, ina shiga ɗoki sosai. Na faɗa a wancan lokacin wannan tawagar ba za ta ba da kunya ba, kuma hakan aka yi…”

“[Argentina] ce tawagar da ta yi nasara kuma a koyaushe tana son ƙara yin hakan. Za mu yi hakan mataki-mataki kamar kullum, amma cike da karsashi, ɗoki, da imani kan abin da muke iyawa."

Rumbun Labarai
Gasar Kofin Duniya: Argentina ta taso daga baya ta doke Masar da ci 3-2, ta kai matakin kwata final
Mbappe ya mayar da martani ga Sanatar Paraguay da ta zagi launin fatarsa
An fitar da Amurka daga gasar Kofin Duniya bayan Belgium ta doke ta da ci 4-1
Trump  ya ce ya kira FIFA kan jan katin da aka bai wa Folarin Balogun
Mece ce Doka ta 27 a kundin ladabtarwar FIFA wadda ta ba danwasan Amurka, Balogun damar dawowa wasa?
Neymar ya yi bankwana da tawagar Brazil bayan Norway ta fitar da su daga Kofin Duniya
Nijeriya ta ce an kashe 'yan ƙasarta biyu a zanga-zangar ƙin jinin baƙi a Afirka ta Kudu
Maroko ta kai ga matakin kusa da daf da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya yayin da Kanada ta fice
Riyad Mahrez ya yi ritaya daga tawagar Algeria bayan fitar da su daga Kofin Duniya
Ronaldo da Ramos sun ci ƙwallo yayin da Portugal ta doke Croatia a Kofin Duniya
Belgium ta cire Senegal daga Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026
NASA ta sha alwashin aika ƙwallon ƙafa zuwa Duniyar Wata idan Amurka ta lashe Kofin Duniya
Norway ta fitar da Ivory Coast daga Gasar Kofin Duniya
Canada ta fitar da Afirka ta Kudu a zagayen 'yan-32 a Gasar Kofin Duniya
Kun san ƙasashen Afirka tara da suka kai zagayen sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Kofin Duniya ta 2026?
FIFA tana cire sunan giya daga Kyautar Gwarzon Wasa da ake bai wa 'yanwasa Musulmi a Kofin Duniya
Antonio Conte ya sake zama kocin Italiya
Wane kasashe biyu ne za su so faduwa wasansu na karshe a rukunin gasar Kofin Duniya?
Cristiano Ronaldo ya zama ɗanwasa na farko da ya zura ƙwallo a raga a Gasar Cin Kofin Duniya shida
Messi ya kafa tarihin yawan cin ƙwallo a Gasar Kofin Duniya yayin da Argentina ta doke Autsria 2-0