Gwamnatin Ghana za ta kawo ƙarshen bincike da ‘yansanda ke yi na ababen hawa a kan hanya daga watan Satumban 2026, yayin da gwamnatin ta gabatar da wani sabon tsari na yanar-gizo don gano waɗanda suka keta doka tare da aiwatar da hukunci kan ababen hawa da aka kama su da laifi.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Ghana, Mohammed Muntaka Mubarak ne ya sanar da matakin a yayin ƙaddamar da wasu jerin Ayyukan Gwamnati a Accra, yana mai cewa a yanzu hukumomi za su sauya daga tsarin sa ido da bincike kai- tsaye zuwa ga amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da bin doka da oda.
‘‘A ƙarƙashin sabon tsarin, za a yi amfani da kyamarorin masu aiki da lanartarki, da na’urar tattara bayanai da ta ɗaukar hoto don gano laifuka a yayin zirga-zirgar ababen hawa, kuma za a haɗa-gwiwa da Sashen Kula da Sufuri da Motoci (MTTD) na ƙasar don cim ma wannan mataki,’’ in ji Ministan.
Ministan ya ƙara da cewa, ba za a riƙa duba takardu da lasisin tuki a zahiri daga masu ababen hawa ba kamar yadda aka saba a yayin binciken ‘yansandan kan hanya, yana mai cewa a madadin haka, direbobi za su gabatar da lambobin lasisinsu ta hanyar intanet a yayin cike bayanansu.
Kyamarori za su yi ɗauki hoto da bidiyon waɗanda ake zargi da keta dokokin kan hanya, yayin da jami'ai a ɗakunan sa ido kan ayyukan da aka keɓe za su tantace bayanan da na’urar ta ɗauka, in ji ministan.
Ya ƙara da cewa, da zarar an tabbatar da laifi, za a tura wa masu ababen hawa saƙo game da laifin da suka aikata ta intanet tare da hukuncin da ya dace.
A cewar Muntaka, an tsara shirin ne don tafiya da zamani tare da inganta fannin sa ido kan zirga-zirgar ababen hawa, da rage jinkiri da kuma taƙaita hulɗa ta kai-tsaye tsakanin jami'an 'yansanda da masu ababen hawa.
Kazalika ya ce, mayar da hankali kan aiwatar da doka ta na’ura zai taimaka wajen rage karɓar cin hanci da rashawa a kan hanyoyi.
Ana sa ran wannan shiri zai samar da gagarumin sauyi a tsarin dokoki kan zirga-zirgar ababen hawa sosai a Ghana ta hanyar maye gurbin bincike a zahiri zuwa ga amfani da nau’urar kyamara da ke sa ido da kuma tabbatar da an bi doka da oda.

















