Tsohon golan Manchester United, Sergio Romero, ya yi ritaya daga kwallo
Tsohon golan Manchester United, Sergio Romero, ɗan asalin Argentina ya yi ritaya daga buga ƙwallo saboda bai wa iyalinsa lokaci.
Sergio Romero, tsohon golan Manchester United ta Ingila, kuma tsohon golan tawagar Argentina, ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa saboda bai wa iyalinsa lokaci.
Mai shekaru 39, Romero ya kasance golan da ya fi kowa tare wa ƙasarsa Argentina raga, har sau 96. Ya bar ƙwallo bayan lashe kofuna da dama cikin shekaru kusan 20 da ya yi a fili.
Ƙungiya ta ƙarshe da ya buga wa wasa ita ce Argentinos Juniors ta Argentina, wadda ya bari a Disamban 2025. A yanzu rahotanni na cewa zai shiga aikin horar da ‘yanƙwallo.
Romero ya bayyana aniyarsa ta shiga harkar horarwa ba tare da ɓata lokaci ba, inda yake alfahari da ƙwarewar da ya samu daga sanannun koci a duniya, irinsu Van Gaal, Jose Mourinho, Tata Martino, da Alejandro Sabella.
Lokacin da yana buga wa Manchester United, Sergio Romero ya kasance zaɓi na biyu bayan babban golan ƙungiyar, David de Gea, amma ya taka rawar gani sosai a gasannin da ya buga.
A 2014, tawagarsa ta Argentina ta zo ta biyu a gasar Kofin Duniya. Sannan shi ne ya kama gola sanda Man United ta lashe kofin FA a 2015-16, ƙarƙashin koci Louis van Gaal.
Ya kuma lashe kofi na biyu mafi daraja a Turai, na UEFA Europa a 2016-17, ƙarƙashin koci Jose Mourinho.